Tuna Baya: Ɗan Kwankwasiyya Ya Ce Wanda Ya Zabi Tinubu, APC ba Shi ba Aljanna
- Tsohon hadimin Gwamna Abba Kabir, Hon. Abba Anas Dala, ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Bola Tinubu a wani tsohon bidiyo
- Ya ce duk wanda ya zabi Tinubu da APC a 2023 “ba zai shiga aljanna ba” saboda goyon bayan abin da ya kira zalunci
- Hon. Dala ya danganta talauci da kashe-kashe a Arewa da salon mulkin APC, yana cewa goyon bayanta kamar yada barna ne a kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben 2027, mun ci karo da wani tsohon bidiyo da ya ke magana game da sake zaben APC da Bola Tinubu a 2023.
Wani tsohon hadimin Gwamna Abba Kabir, Hon. Abba Anas Dala ya yi kakkausar suka ga salon mulkin APC duba da rashin tsaro da ake fama da shi.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano wani bidiyo ne da ke yawo a kafofin sadarwa wanda Hon. Nuhu Sada ya wallafa a shafinsa na X.
Dan Kwankwasiyya ya ja kunne kan zaben Tinubu
A cikin bidiyon, Hon. Dala ya nuna damuwa game da samun kashe-kashe da ake ta yi a Arewacin Najeriya.
Ya koka tare da dura kan wadanda suke ci gaba da goyon bayan gwamnatin da jam'iyyar APC.
Ya ce zai yi wahala wanda zai goyi bayan Tinubu da wanda ya zabe shi da APC a 2023 ya shiga aljanna.
Ya ce:
"Hukuncin da zamu yanke wa duk mutumin da ya sake ya zabi jam'iyyar APC musamman Ahmad Bola Tinubu.
"Duk wanda ya zabi Ahmad Bola Tinubu to ba zai shiga aljanna ba.
"Ai ba zaka shiga aljanna ba, to ka goyi bayan a ci gaba da kashe mutane, a ci gaba da cin zarafin mata."

Source: Facebook
Tinubu: Gargadin da aka yi yan Najeriya
Hon. Dala ya ce maganarsa bata yi tsauri ba ko kadan saboda duk wanda ya goyi bayan zalunci ba zai samu rahama ba.
Ya ce zaben Bola Tinubu da APC kamar sake goyon bayan zalunci ya ci gaba ne a fadin kasa.
"Babu tsauri a magana ta, duk mutumin da ya goyi bayan a ci gaba da yada barna to ba zai samu rahama ba.
"Zaben Ahmad Bola Tinubu da jam'iyyar APC yada barna ne a bayan kasa don haka aljanna ta yi wa mutum nisa.
"Yanzu ga shi ɗan Majalisa ne ya fito yake maganar an kwashe wa al'umma triliyan a bankin kasa kowa yana ji."
Hon. Abba Dala
Hon Dala ya ce shiyasa ya ce zaka ga duk al'umma sun talauce, kowa ya koma roko da bara a Arewa.
Tinubu ya magantu kan murkushe yan adawa
A baya, an ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana mai tsauri kan batun jefarsa da ake yi da zargin yunkurin murkushe adawa a Najeriya.
Tinubu ya bayyana cewa masu sukarsa suna da 'yanci da damar fadin ra'ayoyinsu da albarkacin bakinsu amma ba shi da bindiga a hannunsa da zai kashe su.
Shugaban kasar ya nuna cewa ba zai ga laifin duk wani dan siyasa da ya fice daga jam'iyyar da ke shirin rugujewa ba saboda neman tsira take yi shi ma.
Asali: Legit.ng


