Atiku da Jagororin Adawa a Najeriya Sun Cimma Matsaya kan Sabuwar Dokar Zabe ta 2026
- Jagororin jam'iyyun hamayya a Najeriya sun yi zama kan sabuwar dokar zabe da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu
- A wata sanarwa da suka fitar bayan taron a Abuja, jiga-jigan adawa sun nuna rashin amincewa da dokar zabe ta 2026
- Sun bukaci Majalisar tarayya ta gaggauta fara aikin sake gyara dokar domin ta yi daidai da muradin 'yan Najeriya na samun sahihin zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyun adawa a Najeriya sun yi watsi da dokar zabe ta 2026 wadda Majalisar Tarayya ta amince da ita kwanan nan, kuma Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu.
Jam’iyyun sun yi kira ga Majalisar Tarayya da ta gaggauta fara wani sabon tsari na yi wa dokar kwaskwarima domin cire abin da suka kira "munanan tanade-tanade" da ke cikin dokar.

Kara karanta wannan
Sabon jadawalin zaben 2027 ya fara tayar da kura a Najeriya, ADC ta dura kan INEC

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta ce sun bayyana matsayar tasu ne a yayin wani taron manema labarai mai taken “Kira na Gaggawa domin Ceto Dimokuradiyyar Najeriya,” wanda aka gudanar a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja ranar Alhamis.
'Yan adawa sun yi fatali da dokar zabe ta 2026
A cikin wata sanarwa da Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Ahmed Ajuji, ya karanta bayan taron da suka yi, jagororin adawa sun bayyana cewa:
“Muna bukatar Majalisar Tarayya ta gaggauta fara sabon gyara ga Dokar Zabe ta 2026, domin cire dukkan wasu munanan tanade-tanade da kuma tabbatar da cewa dokar ta yi daidai da muradin ‘yan Najeriya na samun sahihin zabe, kuma adali."
Jagororin adawa da suka halarci taron Abuja
Daga cikin jagororin 'yan adawa da suka halarci taron akwai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma shugaban ADC, David Mark, da tsohon Gwamnan Jihar Osun kuma sakataren ADC, Rauf Aregbesola.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta biya kudi kafin Amurka ta turo sojoji zuwa Najeriya? Hedkwatar tsaro ta yi bayani
Sauran sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, da kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.
Haka kuma shugaban jam'iyyar NNPP na kasa Ahmed Ajuji da sauran manyan mambobin jam'iyyar, musamman Buba Galadima, duk sun halarta.
Shugabannin adawa sun soki APC da Tinubu
Gamayyar jam’iyyun ta ce dokar da Tinubu ya sanya wa hannu tana dauke da wasu sassa da ke "yaki da dimokuradiyya," wadanda suke ganin za su raunana sahihancin zabe da kuma amincewar jama'a ga tsarin kada kuri'a.
Ahmed Ajuji ya zargi jam’iyyar APC da kokarin nuna Shugaba Tinubu a matsayin dan takara daya tilo mai karfi a zaben 2027, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa alkaluman da suke da su sun nuna cewa ana iya tura sakamakon zabe ta na’ura daga kowace rumfar zabe, don haka suna mamakin dalilin da ya sa aka sanya batun tattara sakamako ta takarda a sabuwar dokar zabe.
Har ila yau, ya bayyana mamakinsa kan yadda shugaban kasar ya gaggauta sanya wa dokar hannu, alhali bai yi hakan ga wasu dokokin ba.
Yuauf Kabir Isiya, wani matashin dan ADC ya shaidawa Legit Hausa cewa ta tabbata gwamnati mai ci na neman maida Najeriya kasa da jam'iyya daya ke mulki.
Ya ce babu abin da ke cikin wannan dokar zabe face son rai da juma tsare-tsaren da za su murkushe yan adawa kafin zaben 2027.
"Kai da ganin yadda aka yi gaggawar sa hannu a dokar ka san akwai wata a kasa, don haka muna tare da shugabannin mu, ba gudu ba ja da baya," in ji shi.
Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan El-Rufai
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce gwamnati za ta dauki alhakin duk abin da ya samu Nasir El-Rufai.
Atiku ya fadi haka ne bayan rahotannin da ke cewa El-Rufai ya yi zubar jini daga hanci yayin da yake tsare a hannun hukumar yaki da rashawa watau ICPC.
Ya jaddada cewa lafiya da jin dadin tsohon gwamnan na da muhimmanci ga iyalansa da abokansa, yana mai cewa dole ne a ba ‘yan Najeriya cikakken bayani kan halin da yake ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
