Kwamishina: Yadda Abba Ya Hakura da 60% na Shugabanci a APC
- Kwamishina a gwamnatin Kano, Aliyu Isa Aliyu ya karyata batun rabon mukaman jam'iyyar APC bayan sauya shekar gwamna
- Ya yi magana ne a yayin da ake ruruta cewa an yi rabon mukaman 50/50 tsakanin mutanen gwamna da wadanda ya tarar a APC
- Aliyu Isa Aliyu ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf da kansa ya dauki matakin kawo maslaha a tsakanin yan jam'iyya domin a kai ga ci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kwamishinan bunkasa kiwon dabbobi a Kano, Aliyu Isa Aliyu, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa akwai yarjejeniyar rabon mukamai ko iko na 50/50 a jam’iyyar APC a jihar.
A wata sanarwa da ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne, yana mai cewa tun daga farko an amince ne da tsarin rabon 60/40 tsakanin bangarorin da abin ya shafa.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Aliyu Isa Aliyu ya bayyana cewa dukkanin matakan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauka a kan batun don ci gaban kowa ne.
Kwamishina ya yi maganar rabon mukamai a APC
Aliyu Isa Aliyu ya bayyana cewa a cikin hikimarsa, Gwamna Abba Kabir Abba Yusuf ya amince da a bar wa tsofaffin 'yan APC da kuma kananan hukumomi 60% na mukamai a wasu kananan hukumomi 14.
A kalamansa:
“Labarin da ke yawo game da wata yarjejeniya ta rabon 50/50 a cikin APC ba gaskiya ba ne. Tun daga farko, tsarin da aka amince da shi shi ne 60/40.”

Source: Facebook
Aliyu Isa Aliyu ya kara da cewa Gwamna, cikin hikima ya amince cewa a kananan hukumomi 14, tsohuwar APC za ta karbi 60%.
A cewarsa, haka aka aiwatar da tsarin a dukkannin kananan hukumomin jihar Kano tun bayan da aka amince da shi.

Kara karanta wannan
Halin da tsohon shugaban APC, Oshiomhole ya shiga bayan tsige shi a mulkin Buhari
An yi komai cikin tsari - Kwamishina
A cewar Kwamishinan, ko a cikin tsarin rabon 60/40 din ma, an gudanar da komai cikin tsari da adalci domin tabbatar da cewa kowanne bangare ya samu wakilci yadda ya dace.
Ya ce:
“Ko a cikin tsarin rabon 60/40 din, an aiwatar da komai cikin tsari domin tabbatar da cewa bangarorin biyu sun samu wakilci cikin adalci.”
Aliyu Isa Aliyu ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin da shugabannin jam’iyya suka yi domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da kuma kauce wa duk wata takaddama da ka iya tasowa.
Ya kara da cewa yada labarin rabon 50/50 ba tare da hujja ba, na iya jawo rudani da rashin fahimta a tsakanin 'yan jam’iyya da magoya bayanta.
Don haka ya bukaci jama’a su yi watsi da irin wadannan rahotanni marasa tushe da wasu ke yadawa.
APC ta hana sayawa Tinubu fom
A baya mun wallafa cewa jam'iyyar APC ta yi martani bayan wasu matasa sun hada miliyoyin Naira domin saya wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu fom din takara.

Kara karanta wannan
Rikicin APC: Majalisa ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamna? Aiyedatiwa ya yi bayani
Matasan suna son Tinubu ya sake tsayawa takarar Shugaban kasa a kakar zabe ta 2027 da ke kara matsowa tare da jaddada goyon bayansu ga yadda yake mulkar Najeriya.
Nentawe Yilwatda, Shugaban APC na kasa ya mika godiya ga matasan da suka sayi fom din, sai dai ya gargadi masu yunkurin cewa za su cigaba da yin hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
