Kwankwaso Ya Yi Magana bayan Ganawa da Gwamna PDP, Ya Tabo Abin da Suka Tattauna

Kwankwaso Ya Yi Magana bayan Ganawa da Gwamna PDP, Ya Tabo Abin da Suka Tattauna

  • Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi takaitacciyar magana bayan kammala tattaunawa da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo
  • Kwankwaso ya bayyana cewa yana da kyakkyawar alaka da Gwamna Makinde, wanda ke wa'adinsa na karshe a kan mulki
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da ake yada jita-jitar cewa akwai yiwuwar Gwamna Makinde da Kwankwaso su kulla kawance kafin zaben 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Da yammacin ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairun 2026 aka samu labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde.

Rahotanni sun ce Kwankwaso da Makinde na PDP sun shiga wata tattaunawar sirri a ofishin gwamna da ke gidan gwamnatin Oyo a Ibadan.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an samu karin gwamnan PDP da yan Majalisa da za su koma APC

Gwamna Makinde.
Gwamna Seyi Makinde lokacin da ya karbi bakuncin jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ganawar Kwankwaso da Makinde ta ja hankali

Jaridar Daily Trust ta ce wannan gannawar, wadda aka bayyana a hukumance a matsayin ziyarar ban girma, ta ja hankalin ‘yan siyasa sakamakon rade-raden da ake yi na yiwuwar kulla sabon kawance gabanin zaben 2027.

Kwankwaso ya samu rakiyar shugaban NNPP na kasa, Dr. Ajuji Ahmed; sakataren yada labarai na kasa, Ladipo Johnson; sakataren kwamitin amintattu, Buba Galadima; da sauran manyan jiga-jigai.

Abin da ya kai Kwankwaso jihar Oyo

Tawagar ta NNPP ta ziyarci jihar Oyo ne domin kaddamar da sabon ofishin jam’iyya na jiha da kuma tattauna batutuwan da suka shafi harkokin cikin gida ma jam’iyya.

Sai dai, ziyarar da ya kai wa Makinde, gwamna da ke wa’adi na biyu a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ta ja hankali sosai saboda bambancin jam’iyyun shugabannin biyu.

Tattaunawar sirrin ta dauki tsawon kusan sa’o’i biyu, kuma an yi ta ne ba tare da an bar yan jarida sun shiga don dauko rahoto ba.

Kara karanta wannan

Bayan rasa Abba Kabir a Kano, Kwankwaso ya ziyarci gwamnan PDP har gida

Martanin Kwankwaso bayan ganawa da Makinde

Da yake magana da manema labarai bayan taron, Kwankwaso ya yi watsi da zargin cewa ziyarar tana da alaka da kulla kawance tsakanin jam’iyyun adawa.

A ruwayar Leadership, tsohon gwamnan ya ce:

“Wannan ziyarar ta fi mayar da hankali kan zumunci fiye da siyasar jam’iyya. Ni da Gwamna Makinde mun dade da sanin juna. Kafin mu wuce taron jam’iyyar mu a jihar, na ga ya dace na biyo na gaishe shi.”
Kwankwaso.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Kwankwaso ya kuma waiwayi tarihin siyasarsa, inda ya bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka kafa PDP a 1998, kuma an zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar Kano a 1999 a karkashin jam’iyyar.

Ya tunatar da cewa ya taba yin Ministan Tsaro a gwamnatin PDP, sannan ya sake dawowa matsayin gwamna a 2011, kafin daga bisani ya ahiga APC, sannan kuma ya zama jagoran jam’iyyar NNPP na kasa.

Kwankwaso ya hadu da Gawuna a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu da tsohon dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna.

Kara karanta wannan

2027: Matasa sun yi karo karo, sun tara N100m don saya wa Tinubu fom ɗin takara

Kwankwaso ya hadu da Dr Nasiru Yusuf Gawuna a filin jirgin saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano da ke cikin birnin Kano.

Hakan na zuwa ne bayan madugun Kwankwasiyya ya kai ziyara gidan tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau bisa rasuwar yayansa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262