An Zo Wajen: Gwamna Bala Ya Tsage Gaskiya kan Yiwuwar Ficewa daga PDP
- Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi tsokaci kan yiwuwar ficewa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Sanata Bala Mohammed wanda ake yi wa lakabi da Kauran Bauchi ya bayyana cewa Najeriya na bukatar adawa mai karfi
- Gwamnan ya bayyana cewa mutanen jihar Bauchi sun yi masa abubuwa da dama saboda haka ba zai bar su ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi magana kan yiwuwar barin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar PDP wadda ya lashe kujerar gwamna sau biyu a karkashinta.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Bala ya bayyana hakan ne yayin wani taron buda baki da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 10.
An gudanar da taron ne na buda baki saboda azumin watan Ramadan a gidan gwamnati da ke jihar Bauchi a ranar Talata, 24 ga watan Fabrairun 2026.
Shin Gwamna Bala zai bar PDP?
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ba shi da wani dalilin barin jam’iyyar PDP.
"Idan na bar PDP na koma kowace jam’iyyar siyasa, to ni ba Kaura ba ne, ni matsoraci ne. Shi Kaura ba ya gudu daga fagen fama.”
- Gwamna Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ne kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya bayyana cewa mutanen jihar Bauchi ne suka zaɓe shi a matsayin gwamna har sau biyu, inda ya ƙara da cewa:
“Mutanen jihar Bauchi sun yi mini abubuwa da dama, ba zan yi watsi da su ba saboda kowane irin dalili.”

Source: Facebook
Gwamna Bala zai ci gaba da zama a PDP
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar PDP domin dorewar dimokuraɗiyyar Najeriya, wadda ke buƙatar jam’iyyar adawa mai ma’ana da ƙarfi, yana mai jaddada cewa Najeriya tana amfani da tsarin dimokuraɗiyya na jam’iyyu da dama.
Ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga mambobin jam’iyyar PDP a jihar da su kasance masu jajircewa, goyon baya, da biyayya ga jam’iyyar da kuma gwamnatinsa har zuwa ƙarshen wa’adin mulkinsa, jaridar Leadership ta kawo labarin.
Tsagin Wike ya yi wa Bala martani
A wani martani na gaggawa, kwamitin riƙon ƙarya na PDP a jihar Bauchi mai biyayya ga Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ta bakin Jungudo Haruna Mohammed, ya bayyana cewa gwamnan ba mamban PDP ba ne.
Junguno Haruna Mohammed ya dage kan cewa an riga an kori Gwamna Bala Mohammed tare da takwarorinsa na jihohin Oyo da Zamfara da sauran mambobi daga jam’iyyar.
Ya bayyana cewa matsayar jam’iyyar game da korar gwamnan har yanzu tana ba ta canza ba.
Gwamna Bala zai hada gwiwa da harin
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana shirinsa na yin aiki tare da kasar Iran.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa wani kamfanin Iran na shirin kafa babban aikin hako ma'adinai a jihar Bauchi.
Ya jaddada cewa kamfanin ba wai kawai zai ɗauki albarkatun ƙasa ya tafi da su ba ne, zai samar da cikakken tsari da zai daga darajar masana’antu a cikin jihar.
Asali: Legit.ng

