2027: Tinubu Ya Tura Jakadu Lungu da Sako, za Su Isar da Sako ga 'Yan Najeriya

2027: Tinubu Ya Tura Jakadu Lungu da Sako, za Su Isar da Sako ga 'Yan Najeriya

  • Jakadun shugaban kasa Bola Tinubu da ake kira ‘Renewed Hope Ambassadors’ sun gudanar da taro na musamman a fadar shugaban kasa
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci su isar da sakon nasarorin da ya samu a lungu da sakon Najeriya domin a san hakikanin me yake faruwa
  • Taron da tawagar shugaban kasar ta gudanar ya samu halartar manyan mutane ciki har da Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci tawagar ‘Renewed Hope Ambassadors’ da su kai saƙon gyare-gyaren da gwamnatinsa ke yi ga 'yan kasa domin a fahimci manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa.

Shugaban kasar ya jaddada cewa babu wani gyara da zai yi nasara ba tare da jama'ar kasa sun fahimci hakikanin inda aka dosa ba.

Kara karanta wannan

Babu wasa: Tinubu ya tara gwamnoni, ya gaya masu shirinsa don magance rashin tsaro

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima na jawabi
Kashim Shettima na jawabi ga jakadun Tinubu. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Kashim Shettim da ya wakilci Bola Tinubu a wajen taron ya yi karin bayani game da tattaunawar da suka yi a wani sako da ya wallafa a X.

Ayyukan da ke gaban jakadun Tinubu

Yayin da yake bayyana ƙalubalen da ke gaban jakadun, wakilin Tinubu ya ce aikin da ke gabansu shi ne bayyana wa ’yan Najeriya abin da gwamnatin ke yi domin samun karbuwa.

The Nation ta rahoto ya ce:

“Wannan dandali zai zama wata hanya ta hulɗa da jama’a, domin mu kai saƙon cigaban ƙasa zuwa kowace mazaba, kowace al’umma, da kowane lungu da saƙo na ƙasarmu.”

Shugaban ya buƙaci jakadun da su bayyana dalilin da ya sa aka ɗauki wasu matakai masu wuya da kuma yadda za su haifar da ayyukan yi, tsaro, bunkasa kasuwanci da makoma mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa:

“Dole ne su ƙaryata ƙarya da hujjoji, su maye gurbin jita-jita da gaskiya, tare da tabbatar da cewa ’yan Najeriya daga kowane sashi na ƙasa sun samu damar sanin gaskiya.”

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya fada wa Abba da sauran gwamnoni a wurin buda baki a Abuja

Bugu da kari ya buƙaci jakadun da kada su tsaya a wuraren taro, yana so su shiga kan al'umma kai tsaye a mazabu, kasuwanni, gonaki da cibiyoyin ilimi.

Bayanin wasu 'yan APC a taron

Shugaban Jam’iyyar APC, Farfesa Netanwe Yilwatda ne ya jagoranci taron da ya hada gwamnoni, ministoci, ’yan majalisar kasa, shugabannin jam’iyya da kuma wasu shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu.

Yayin da yake hasashe kan 2027, Yilwatda ya ce zaɓen 2027 zai zama gwajin tasirin gyare-gyaren gwamnati da kuma jarumtar da shugaba Bola Tinubu ya nuna.

Da yake yaba wa Tinubu kan yadda bai kunyata 'yan ƙasa ba, Hope Uzodimma ya ce ’yan Najeriya da dama na iya shaida cewa gyare-gyaren na haifar da sakamako mai kyau.

Kashim Shettima da shugabannin APC a Abuja
Kashim Shettima na gaisawa da gwamnan Imo a fadar shugaban kasa. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Kakakin Majalisar Wakilai, Abbass Tajudeen, ya bayyana dalilin da ya sa Majalisar kasa ta mara wa Tinubu baya, yana cewa haɗin gwiwarsu za ta tabbatar da gaskiya, riƙon amana a Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya yabi Aisha Buhari

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed ya taya uwargidan tsohon shugaban kasa, Aisha Buhari murnar cika shekara 55.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: APC ta hana saya wa Tinubu fom din takarar 2027

Bola Tinubu ya bayyana cewa Aisha Buhari mace ce mai tsayuwar daka kan manufofin da ta sa a gaba domin cimma su a rayuwarta.

Ya yaba mata bisa cewa ta kawo cigaba sosai a matakai daban-daban da kuma tallafawa 'yan Najeriya da dama a karkashin gidauniyarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng