Rahoto: Yadda APC Ta Yi Kaca Kaca da Ƴan Adawa a Zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

Rahoto: Yadda APC Ta Yi Kaca Kaca da Ƴan Adawa a Zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

Zaɓukan da aka gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairu a Abuja, Kano da Rivers, sun kafa tarihi a matsayin gwaji na farko ga sabuwar dokar zaɓe ta shekarar 2026.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa dokar hannu ne a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu, kwanaki uku kacal kafin INEC da gudanar da zaɓukan.

Jam'iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zabukan Abuja, Kano da Rivers.
Tutar APC a wani gangamin jam'iyyar da aka gudanar. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Sabuwar dokar zabe ta 2026

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa wannan sabuwar doka za ta bai wa dimokuraɗiyya damar bunƙasa yadda ya kamata a ƙasar nan, in ji rahoton The Cable.

Shi ma Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya goyi bayan hakan inda ya ce gyare-gyaren dokar za su bai wa hukumomi damar gudanar da zaɓuka cike da adalci.

Legit Hausa ta tattaro yadda jam'iyyar APC ta yi kaca kaca da 'yan adawarta a zabukan Abuja, Kano da Rivers, karkashin sabuwar dokar zabe ta 2026:

Kara karanta wannan

Bayan ICPC, El Rufai ya maka hukumar DSS a kotu, ya gabatar da manyan bukatu 3

1. Sakamakon zaɓen ciyamomi a Abuja

A birnin tarayya Abuja, an gudanar da zaɓen ne a kananan hukumomin birnin guda shida. An zaɓi ciyamomi shida da kuma kansiloli 62 waɗanda za su jagoranci al'amuran yau da kullum na mazauna birnin.

Sakamakon da jami'an hukumar INEC suka sanar ya nuna cewa jam'iyyar APC ta samu gagarumar nasara a kusan dukkanin yankunan.

  • Karamar hukumar Abaji

A ƙaramar hukumar Abaji, Abubakar Abdullahi na APC ya sake samun nasara bayan ya samu ƙuri'u 15,535 yau. Ya doke ƴan takarar jam'iyyar YPP da PDP waɗanda suka zo na biyu da na uku.

  • Karamar hukumar Kwali

A ƙaramar hukumar Kwali, Daniel Nuhu na APC ya samu gagarumar nasara da ƙuri'u 17,032. Babban abokin hamayyarsa, Haruna Pai na PDP, ya samu ƙuri'u 8,575 kacal.

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa jam'iyyar APC ta lashe dukkanin mazaɓun dake cikin wannan ƙaramar hukuma.

  • Karamar hukumar Bwari

Haka lamarin yake a ƙaramar hukumar Bwari, inda Joshua Ishaku na APC ya lashe kujerar shugabanci da ƙuri'u 18,466.

Kara karanta wannan

Barau Jibrin ya fito da alamun nasarar Tinubu, Abba da sauran 'yan APC a 2027

  • Karamar hukumar AMAC

Jam'iyyar APC ta kuma lashe zabe a karamar hukumar AMAC, wadda ita ce mazaɓa mafi girma da muhimmanci a Abuja.

Christopher Maikalangu na APC ne ya sake lashe zaɓen, wanda hakan ke nuna ƙarfin jam'iyyar a tsakiyar birnin tarayya.

  • Karamar hukumar Kuje

A ƙaramar hukumar Kuje kuma, Danjuma Samuel na APC ya samu ƙuri'u 17,269, wanda ya ba shi damar doke 'yan takarar PDP, APGA da sauransu.

2. Sakamakon zaɓen cike gurbi a Kano

Jam'iyyar APC ta lashe kujeru 2 na majalisar dokokin jihar Kano da aka gudanar.
Majalisar dokoki a yayin da ake zama a jihar Kano. Hoto: Ibrahim Gudaji
Source: Facebook

A jihar Kano ma, jam'iyyar APC ta samu nasara a duka kujeru biyu na majalisar dokokin jihar da aka fafata a kai, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.

Hukumar INEC ta gudanar da zaɓen ne a mazaɓun Kano Municipal da Ungogo domin cike gurbi bayan rasuwar ƴan majalisar mazaɓun.

Farfesa Ibrahim Tajo Sirajo, babban jami'in zaɓe na birnin Kano, ya bayyana Aliyu Nabil Daneji na APC a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'u 7,484 a mazabar.

Kara karanta wannan

Babban jami'in gwamnatin Amurka zai dura a Najeriya kan batun ta'addanci

A mazaɓar Ungogo kuwa, Farfesa Ali Tijjani Abdullahi ne ya bayyana Aminu Sa’ad Sa’ad na APC a matsayin zakara. Ya doke wasu ƴan takara takwas da ƙuri'u 8,975.

4. Sakamakon zaɓen jihar Rivers

Duk da rahotannin cewa masu jefa ƙuri'a ba su fito da yawa ba kuma an kai kayan zabe a makare, APC ta lashe kujerun majalisar jiha guda biyu a Rivers.

Legit Hausa ta rahoto cewa zaɓen ya gudana ne a mazaɓun Ahoada ta Gabas II da Khana II.

A mazaɓar Khana II, Henrietta Bulabari ta APC ta yi nasara da ƙuri'u 7,647. Ta doke ƴan takara daga jam'iyyun African Alliance, NNPP, YPP da ZLP yau.

A mazaɓar Ahoada ta Gabas II kuma, Ukalikpe Napoleon na APC ya samu nasara da ƙuri'u 3,980, kamar yadda INEC ta sanar.

Martanin Tinubu kan zabukan cike gurbi

A wani labari, Legit Hausa ta rahoto cewa Shugaba Bola Tinubu ya nuna gamsuwarsa da yadda aka gudanar da zaɓukan Abuja, Kano da Rivers cikin lumana.

Cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya taya waɗanda suka yi nasara murna tare da neman su gudanar da mulki cikin adalci da kishin ƙasa.

Shugaban ya kuma jinjina wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, yana mai bayyana cewa nasarar APC a Abuja tana da alaƙa da ayyukan da Wike ya shimfiɗa a birnin

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com