"Ba Mu Yi, Ba Mu Yi," 'Dan Majalisar Tarayya Ya Sha da Kyar da Matasa Suka Yi Kansa a Kano
- Mutane sun fatattaki 'dan Majalisar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe, daga wurin taron APC a mazabarsa
- Bayanai sun nuna cewa tun da dan Majalisar ya ci zaben 2023, bai sake zuwa mahaifarsa Tofa ba sai a wannan karon da zabe ya kusa
- Fustattun matasa sun rika masa ihu a wajen taron, lamarin da ya tilasta wa jami'an tsaro da magoya bayansa fitar da shi a mota
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Matasa sun yi wa dan majalisa wakilai mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe, ihun bama yi tare da korarsa daga wurin taron APC.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wurin taron mazaba na zaben shugabannin jam'iyyar APC a karamar hukumar Tofa da ke Jihar Kano.

Kara karanta wannan
El Rufa'i ya shiga mugun hali hannun ICPC, jini ya rika zuba ta hancinsa ana azumi

Source: Facebook
Yadda matasa suka fatattaki 'dan Majalisa
Daily Trust ta tattaro cewa wasu bidiyoyi da ke yawo a kafafen sadarwa sun nuna gungun matasa suna fadin "ba mu yi, ba mu yi," tare da tunkarar wurin da 'dan Majalisar yake.
Lamarin ya faru ne yayin da Jobe yake jawabi a wurin taron wanda ya gudana garinsu na haihuwa, wato Tofa.
A daya daga cikin bidiyoyin, wanda Aminiya ta wallafa a Facebook, an ji muryar wani daga cikin taron yana cewa, "Wallahi akwai gyara. Mu maharba ba ka dube mu ba."
Sai dai lamarin ya rincabe ne yayin da wasu matasa suka ci gaba da ihu da fadin kalaman batanci.
'Dan Majalisa ya sha da kyar a Kano
Bidiyoyin sun nuna yadda hadimai, jami'an tsaro da magoya baya suka yi kokarin fitar da dan majalisar daga wurin taron a cikin mota.
A farkon wannan watan, Jobe ya nemi afuwar al'ummar mazabarsa kan duk wani kuskure da ya yi a lokacin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, taron da rahotanni suka ce ya kare cikin hargitsi.

Kara karanta wannan
An fara fahimtar wadanda APC za ta zaba shugabannin jam'iyya na kasa a babban gangami
An ruwaito cewa kujerar majalisar wakilai ta Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa tana fuskantar zazzafar siyasa gabanin babban zabe mai zuwa, inda aka ce wasu fitattun jiga-jigan APC suna neman wannan kujera.
Kalubalen da ke gaban Hon. Jobe
Jobe, wanda a halin yanzu yake wa’adi na biyar a Majalisar Wakilai, an ce yana da kudirin neman wa’adi na shida.
Komawarsa jam'iyyar APC kwanan nan ta ruruta jita-jitar cewa yana kokarin ganin ya samu tikitin takara kai tsaye a zabe mai zuwa.
An bayyana cewa taron na Tofa shi ne karon farko da 'dan majalisar ya je garinsu tun bayan da ya lashe zaben wa'adi na biyar a shekarar 2023.

Source: Getty Images
Wannan mazaba dai ta dade tana fitar da fitattun 'yan siyasa, wadanda suka hada da marigayi Danmasanin Kano, Dr. Yusuf Maitama Sule; da marigayi Dr. Maikano Rabiu.
Sauran sun hada da marigayi Mustapha Janguza; Engr. Hamisu Abubakar Lambu; da kuma Hon. Shehu Haruna Lambu.
NNPP ta yi zargin kama 'ya'yanta a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta yi Allah-wadai da kama daya daga cikin 'ya'yanta, Aiha K. Nass, da hukumomin tsaro suka yi a Kano.

Kara karanta wannan
Bayan abin da EFCC, DSS suka yi wa El Rufai, na kusa da Peter Obi ya fadi fargabar ubangidansa
Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar NNPP a Kano, Injiniya Ibrahim Karaye, ya ce wannan abin takaici ne, kuma ya saba wa tsarin dimokuradiyya.
NNPP ta bukaci a saki Aiha K. Nass ba tare da ɓata lokaci ba saboda ‘yan kasa na da ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma ‘yancin shiga kungiyoyi ko jam’iyyun siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng