Bayan Pantami, Malamin Musulunci Sheikh Bashir zai Fito Takarar Gwamna a 2027
- Malamin Musulunci, Sheikh Bashir Sani Sokoto ya bayyana cewa ya shirya maganar takarar gwamna kamar Sheikh Isa Ali Pantami
- Sheikh Bashir Sani Sokoto ya bayar da labarin dalilan da suka sa ya yanke shawarar yin takara bayan cewa ba zai yi ba a sau da dama
- Ya yi magana ga jami'an tsaro dangane da kariyar da suka ce za su ba shi game da barazanar kai hare-hare da ya ce yana fuskanta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya bayyana cewa ya sauya matsaya game da batun siyasa, zai yi takarar gwamnan jihar Sokoto.
Malamin ya bayyana haka ne a wani wa'azi da ya gabatar, inda ya ce ba gudu ba ja da baya a shiga harkar siyasa a Najeriya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da malamin ya yi ne a wani bidiyo da Taskar Malaman Sunnah TV ta wallafa a shafin YouTube.
Sheikh Bashir zai yi takarar gwamna
Malam Bashir Sani Sokoto ya bayyana cewa zai yi takarar gwamna a Sokoto ne yayin da ya yi korafi game da barazanar da ya ke fuskanta.
Ya ce:
"Na fada cewa ba zan yi takara ba ya fi sau 100 amma sun ki yarda. To daga yau, ku ji daga bakina, na sauya ra'ayi, zan yi takarar."
Masu sauraro sun barke da kabbarori a lokacin da Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya yi wannan maganar, inda ya rika kira da a saurara.
Ya cigaba da cewa:
"Tun da dai na ce ba ni yi amma bai wadatar ba, to na ce zan yi, sama ta fado ko a yi girgizar kasa."
Wani sako da aka wallafa a shafin malamin na Facebook ya tabbatar da cewa tura ta kai bango kuma ya shirya fita takara a jihar Sokoto.
Maganar malamin kan 'yan sanda
Malamin ya mika godiya ga shugaban 'yan sandan yankin (DPO) game da kariyar da ya ce za a ba shi wajen tabbatar da yana lafiya.
Amma daga lokacin da ya yi wa'azin, ya ce ba shi da bukatar kariya daga DPO, sufeton 'yan sanda ko ma wani jami'in tsaro a kasar nan.
Bugu da kari, malamin ya bayyana cewa rayuwarsa a hannun Allah ta ke kuma ya godara da shi, ya ce yana jiran masu masa barazana su dawo.

Source: Facebook
Ya kara da cewa akwai wanda ya shiga gidansa amma da ya haska fitila sai mutumin ya fita da gudu bayan sun fafata da shi.
Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya ce ba ya zargin kawo da kawo masa hari, sai dai ya ce ya san saboda siyasa ake shirya masa makarkashiya.
Pantami zai yi takarar gwamna
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa zai yi takarar gwamna a jihar Gombe.
Sheikh Pantami ya bayyana cewa mutane da dama sun nemi ya fito takara, tun yana kin abin a ransa har ya ji ya fara gamsuwa.
A kokarin da ya yi wajen neman dacewar Allah, Malam Isa Ali Pantami ya bayyana cewa ya roki zabin Ubangiji a dakin Ka'aba.
Asali: Legit.ng


