2027: Matasa Sun Yi Karo Karo, Sun Tara N100m don Saya wa Tinubu Fom ɗin Takara

2027: Matasa Sun Yi Karo Karo, Sun Tara N100m don Saya wa Tinubu Fom ɗin Takara

  • Matasan Kogi sun tara N100,000,000 domin saya wa Shugaba Bola Tinubu fom din takarar shugaban kasa na zaben shekarar 2027
  • Gwamna Ahmed Ododo ya mika kudin ga shugaban jam'iyyar APC na kasa inda ya bayyana hakan a matsayin nuna goyon baya ga shugaban yau.
  • Shugaban jam'iyyar APC ya bayyana cewa matasan Kogi sun kafa tarihi inda ya ce babu bukatar sake karbar kudin fom daga kowa yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kogi - Wata ƙungiyar matasa daga jihar Kogi ta tara jimillar N100m domin saya wa Shugaba Bola Tinubu fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, ne ya miƙa wannan kuɗi ga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a birnin Abuja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Kano: Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jawo tarnaki a jam'iyyar APC

Matasa sun ba da N100m ga APC don a saya wa Tinubu fom din takara a 2027
Gwamna Usman Ododo (tsakiya) yana mika N100m da matasan Kogi suka tara don saya wa Tinubu fom din takara a 2027 ga shugaban APC na kasa. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Matasa sun tara kudin fom din takarar Tinubu

Duk da cewa Tinubu bai riga ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara ba, wannan mataki na matasan Kogi ya nuna irin kwarin gwiwar da suke da shi kan salon jagorancinsa, in ji rahoton Punch.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko a tarihin ƙasar nan da matasa za su fito su ce suna son saya wa shugaba fom maimakon su nemi wani abu daga gare shi.

A cewarsa, matasan sun bayyana cewa yanayin da ake ciki ya nuna cewa tattalin arziƙin ƙasar yana samun ci gaba mai kyau a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

"Sun gode wa shugaban kan ba wa ƴan asalin jihar Kogi manyan mukamai, ciki har da babban hafsan sojojojin kasa da kuma shugaban hukumar INEC."

- Nentawe Yilwatda.

Sanarwar rufe karɓar kuɗin fom

Wani rahoto da hadimin shugaban APC, Imran Muhammad ya wallafa a shafinsa na X, ya nakalto Farfesa Yilwatda yana cewa wannan mataki na matasan Kogi ya zama misali ga dukkan matasan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan kashe kashe a taron APC, ya dauki kwakkwaran mataki

Ya ƙara da cewa, duk da cewa akwai wasu kungiyoyin da suka yi alƙawarin bayar da tallafi, matasan Kogi ne kawai suka kawo kuɗin a hannu.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana:

"Ina so in sanar da cewa babu wanda ya kamata ya sake damun kansa wajen kawo kuɗin sayen fom ɗin Shugaba Tinubu, domin matasan Kogi sun riga sun biya kuɗin fom ɗin tun kafin lokaci ya yi."

Wannan yunƙuri ya samu goyon bayan jam’iyyar APC, ƙungiyar gwamnoni da kuma kwamitin zartarwa na ƙasa, waɗanda duk suka amince da marawa Tinubu baya a zaɓen 2027.

Shugaban APC ya ce yanzu babu bukatar wata kungiya ta saya wa Tinubu fom, matasan Kogi sun riga sun saya.
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda yana jawabi bayan matasan Kogi sun ba da N100m na kudin fom din takarar Tinubu. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Tasirin sayawa Tinubu fom ga jihar Kogi

Shugaban jam'iyyar ya jaddada cewa Shugaba Tinubu da Gwamna Ododo sun tabbatar da cewa matasa su ne shugabannin gobe ta hanyar ba su damar shiga cikin gwamnati a dama da su tun yanzu.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum suna ganin wannan a matsayin wani salon siyasa da zai kara kimar Gwamna Ahmed Ododo da kuma mutanen Jihar Kogi a idon fadar shugaban ƙasa.

Barau ya hasasho nasarar Tinubu

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Jam'iyyar ADC ta taso Tinubu a gaba, ta fadi shirin da take yi don hana magudi

A wani labari, mun ruwaito cewa, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana game da makomar APC a zaben 2027.

Sanata Barau Jibrin ya magantu ne bayan nasarar da jam'iyyar ta samu a zabukan da aka yi a Rivers, Kano da birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewa hakan alama ce da ke nuna cewa Shugaba Bola Ahmad Tinubu, Abba Kabir Yusuf da 'yan APC za su yi nasara a zabukan 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com