'An Tafka Magudi,' PDP Ta Dauki Babban Mataki da Ta Rasa Kujeru 5 a Zaben Abuja

'An Tafka Magudi,' PDP Ta Dauki Babban Mataki da Ta Rasa Kujeru 5 a Zaben Abuja

  • Jam'iyyar PDP ta kafa tawagar lauyoyi karkashin domin kalubalantar nasarar da jam'iyyar APC ta samu a kananan hukumomi biyar na Abuja
  • Hukumar INEC ta bayyana cewa jam'iyyar APC ce ta lashe AMAC da Bwari da Abaji da Kwali da kuma Kuje a zaben na ranar Asabar
  • PDP ta yi zargin cewa ta samu bidiyo da ya nuna an yi amfani da jami'an tsaro wajen aikata laifuffukan zabe da tursasa masu jefa kuri'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam'iyyar PDP ta ƙaddamar da wata tawagar lauyoyi ta musamman domin ƙalubalantar sakamakon zaɓukan ƙananan hukumomin birnin tarayya Abuja da aka gudanar ranar Asabar.

Kamar yadda hukumar INEC ta bayyana, jam'iyyar APC ce ta lashe kujeru biyar cikin shida, yayin da PDP ta samu kujera ɗaya kacal a zaben.

Kara karanta wannan

Barau Jibrin ya fito da alamun nasarar Tinubu, Abba da sauran 'yan APC a 2027

Jam'iyyar PDP ta shirya kalubalantar sakamakon zaben ciyamomin Abuja
Tanimu Turaki, shugaban PDP na kasa na jawabi ga 'yan jarida bayan ganawa da Goodluck Jonathan a Abuja. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Matakin PDP na kalubalantar sakamakon zaben na kunshe ne a cikin sanarwar da jam'iyyar ta fitar a shafinta na X a ranar 22 ga Fabrairu, 2026.

Sakamakon zaben ciyamomi a Abuja

Tawagar lauyoyin, ƙarƙashin jagorancin babban lauyan jam'iyyar na ƙasa, Shafi Bara’u, za ta binciki zarge-zargen maguɗi da tursasa masu jefa ƙuri'a da aka tafka a ranar Asabar.

Hukumar INEC ta sanar da cewa jam'iyyar APC ta mamaye kusan dukkanin kananan hukumomin birnin tarayya, inda ta samu nasara kamar haka:

Ƙaramar hukuma

Zaɓaɓɓen shugaba (APC)

Ƙuri'un da ya samu

AMAC

Christopher Maikalangu

40,295

Bwari

Joshua Ishaku

18,466

Abaji

Umar Abubakar

15,535

Kwali

Nuhu Daniel

17,032

Kuje

Danjuma Shekwolo

17,269

PDP ta taya dan takararta murna

A ɓangare guda, jam'iyyar PDP ta samu nasara ne kawai a ƙaramar hukumar Gwagwalada, inda Mohammed Kasim ya zama zaɓaɓɓen shugaba, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.

Jam'iyyar PDP ta taya Kasim murna, tana mai bayyana nasarar tasa a matsayin wadda aka samu cikin yanayi na tsangwama da siyasar kuɗi.

Kara karanta wannan

Kuje: Hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben ƙananan hukumomi a Abuja

Sanarwar ta ce:

"Kwamitin NWC na jam'iyyar PDP na taya dan takararta murna bayan samun nasara a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a Abuja a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.
"Wannan nasara, wacce aka samu duk da karancin masu kada kuri'a, ta zamo abin alfahari la'akari da cewa an samu yanayi na tsangwama, amfani da kudi da magudin zabe mafi muni."
Jam'iyyar PDP ta ce an samu magudin zabe da sayen kuri'u a zaben Abuja.
Wasu jami'an hukumar INEC suna kidaya kuri'un da aka kada a zaben 2023. Hoto: BENSON IBEABUCHI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Zargin maguɗi a zaben Abuja

Sakataren yaɗa labarai na PDP na ƙasa, Ini Ememobong, ya fitar da sanarwa ranar Lahadi inda ya yi zargin cewa an yi amfani da jami'an tsaro wajen ƙwace takardun sakamakon zaɓe.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda jama'a ba su fito zaɓe ba, wanda ya ce hakan ya faru ne saboda rashin amincewa da sabuwar dokar zaɓe ta 2026.

Ini Ememobong ya bayyana:

"Hotunan bidiyo sun nuna yadda aka yi amfani da jami'an tsaro dauke da makami wajen karkatar da sakamakon zaɓe a rumfuna daban-daban."

Kara karanta wannan

An buga ta: INEC ta sanar da sakamakon zaben karamar hukumar birnin Abuja

Jam'iyyar ta bayyana cewa wannan zaɓen ƙananan hukumomin ya zama tamkar manuniya kan abin da zai faru a babban zaɓen shekarar 2027 idan har ba a yi gyara cikin gaggawa ba.

Yadda APC ta lashe zabe a Kwali

A wani labari, mun ruwaito cewa, INEC, ta sanar da wanda ya lashe zabe a karamar hukumar Kwali da ke birnin tarayya Abuja.

Daniel Nuhu na jam’iyyar APC ne ya lashe zaɓen shugabancin ƙaramar hukumar Kwali da ƙuri’u 17,032, a cewar hukumar INEC.

Nuhu ya samu nasara ne a mafi yawan mazabu inda ya doke Haruna Pai na jam’iyyar PDP, wanda ya samu ƙuri’u 8,575 kacal a zaɓen na ranar Asabar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com