Dan Agundi: Adadin Mutanen da za Su Mutu a Zaben Cike Gurbi da Abba bai Koma APC ba

Dan Agundi: Adadin Mutanen da za Su Mutu a Zaben Cike Gurbi da Abba bai Koma APC ba

  • Jigo a APC reshen Kano, Baffa Babba ‘Dan Agundi ya ce sauya sheƙar gwamnan Kano zuwa cikinsu ya kawo zaman lafiya a siyasar jihar
  • Ya yi gargadin cewa da Abba Kabir Yusuf bai sauya sheka ba, za a iya samun asarar rayuka sama da 1,000 a zaɓen da aka gudanar a ƙarshen mako
  • ‘Dan Agundi ya tabbatar da cewa za su ci gaba da ba gwamnan da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya da hadin kai domin ci gaban Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Jagora a APC reshen Kano, Baffa Babba ‘Dan Agundi, ya bayyana cewa sauya sheƙar gwamnan jihar zuwa jam’iyyar ya taimaka wajen dakile tashin-hankali da zai iya aukuwa a lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

Barau ya fito da alamun nasarar Tinubu, Abba da sauran 'yan APC a 2027

Ya bayyana haka ne a yayin zaɓen cike gurbi da ya gudana a ƙananan hukumomin Birnin Kano da Ungogo a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2026.

Baffa Babba Dan Agundi ya ce siyasar Kano ta samu lafiya
Jigo a APC, Baffa Babba Dan Agundi (hagu), Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Hoto: Muslihu Adam Hassan/Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A wani bidiyo da Premier radio ta wallafa a shafin Facebook, Baffa Babba Dan Agundi gode wa Allah Madaukakin Sarki a kan hikimar da ya bai wa gwamnan Kano.

Dan Agundi ya ji daɗin sauya sheƙar Abba

A bidiyon, Baffa Babba Dan Agundi ya yi godiya ga Allah SWT da ya ba Abba Kabir Yusuf damar yanke shawarar komawa APC, yana mai cewa hakan ya rage yiwuwar rikici mai muni a siyasar jihar.

Ya ce:

“A yau muna gode wa Allah Subhanahu wa Ta’ala bisa hikimar da Ya ba wa mai girma gwamnan jihar Kano na komawa APC.”

Ya ƙara da cewa mutane da dama sun fahimci muhimmancin matakin da gwamnan ya ɗauka, musamman duba da irin zafin takarar da ake sa ran za ta faru kafin sauyin sheƙar.

“Aƙalla a yau, kowa zai fahimci abin da nake nufi. Idan da bai koma APC ba, da za mu iya ganin asarar rayuka sama da 1,000 sakamakon wannan zaɓe, domin da ana takara mai zafi.".

Kara karanta wannan

Kano: Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jawo tarnaki a jam'iyyar APC

Dan Agundi: Sauya sheƙar Abba ta taimaki Kano

A cewarsa, sauyin sheƙar ya kawo ƙarshen duk wata takaddama ko hamayya mai tsanani da ka iya janyo tashin-hankali, yana mai cewa a halin yanzu babu wata gasa mai ƙarfi face ta APC kaɗai.

Ya ce:

“Yanzu da ya koma APC, babu wata takara. APC kaɗai ce. Don haka muna gode wa Allah bisa wannan shawara. Muna farin ciki. Muna gode wa Allah."

Baffa Babba Dan Agundi ya kuma tabbatar da cewa su a matsayinsu na ‘yan jam’iyya za su ci gaba da ba wa gwamnan Kano cikakken goyon baya domin tabbatar da ci gaba a jihar.

Baffa Babba Dan Agundi ya gode wa Allah da Abba ya koma APC
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ya ce:

“Za mu ci gaba da ba gwamna haɗin kai. Haka nan za mu ci gaba da ba shugaban ƙasa haɗin kai domin mu ga mun matsa gaba.”

Ya bayyana cewa haɗin kai tsakanin shugabanni a matakin jiha da na tarayya zai taimaka wajen kawo zaman lafiya, ci gaba da bunƙasa tattalin arziki da kuma tabbatar da tsaro a Kano.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya ankarar da Tinubu kan masu sauya sheka, ya fadi masu yanke makomarsa a 2027

INEC ta fadi sakamakon zaɓen Kano

A baya, mun wallafa cewa APC ta lashe zaben kujerun Majalisar dokokin jiha na mazabun Ungogo da birnin Kano a zaben cike gurbi na ranar Asabar.

INEC ta ce an sami karancin masu kada kuri'a sakamakon azumin Ramadan da kuma rashin shigar manyan jam'iyyun adawa a fafata da su a zaɓen 21 ga watan Fabrairu, 2026.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta yaba wa mazauna Kano bisa gudanar da zaben cikin lumana ba tare da samun wani tashin hankali a lokutan jefa kuri'a ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng