Yaron Sheikh Gumi Zai Yi Takara a Kaduna, Ya Fadi Kujerar da Yake Hari a 2027
- Ɗan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, wato Mubarak Ahmad-Gumi, ya ayyana tsayawa shirinsa na neman takara
- Mubarak ya ce zai yi takara ne a karkashin jam’iyyar APC domin wakiltar mazabar Doka/Gabasawa a majalisar dokokin Kaduna
- A ganinsa, ya kamata matasa su daina tsaya wa a kafafen sada zumunta, su shiga siyasa domin kawo sauyi mai ma’ana a cikin al'umma
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Mubarak Ahmad-Gumi, ɗan malamin addinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a zaben mai zuwa.
Mubarak wanda mahaifinsa ya saba jawo abin magana ya ce ya shirya neman kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a zaben 2027 da ke ƙara tunkaro wa.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Source: Facebook
A hirarsa da Premium Times, Mubarak ya bayyana cewa zai nemi kujerar ne a karkashin APC domin wakiltar mazabar Doka/Gabasawa a jihar Kaduna.
Yadda ɗan Sheikh Gumi ya shirya shiga siyasa
A hirar, Mubarak ya ce shawarar neman takarar ta biyo bayan rokon al’ummar yankin da suka nemi ya fito ya wakilce su a majalisar dokoki.
A halin yanzu, Mubarak na aiki a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin majalisa ga Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
Ya ce kwarewarsa a majalisa ta ba shi damar fahimtar yadda ake tsara dokoki da kuma tasirin manufofi ga talakawa ta yadda za su amfana.
Ya ce:
“Kwarewata a majalisa ta sa na fahimci yadda ake kirkirar dokoki da yadda manufofi ke shafar rayuwar jama’a. Wakilci mai inganci yana da matukar muhimmanci.”
Shawarar Mubarak Ahmad Gumi ga matasa
Mubarak Ahmad Gumi ya bayyana siyasar Najeriya a matsayin wuri da tsofaffi da matasa za su haɗu domin ci gaban jama'a.
A cewarsa, lokaci ya yi da za a hada hikimar dattawa da kuzarin matasa domin samar da shugabanci mai inganci da jama'a za su ji dadinsa.

Source: Original
Ya ce matasan Najeriya suna da kwarewa a fasahar zamani, suna amfani da bayanai da kuma sababbin dabaru wajen warware matsaloli.
A cewarsa, idan ana son sauyi na gaskiya, dole ne matasa su wuce tattaunawa a shafukan sada zumunta su shiga takara da bada gudunmawa kai tsaye.
Mubarak ya kammala digirin farko a jami’ar Sharjah da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.
A yanzu haka yana karatun digiri na biyu a fannin nazarin bayanai da kididdiga a Jami’ar Tsaro ta Najeriya da ke Kaduna.
Ya jaddada cewa bai kamata a takaita siyasa ga wasu tsiraru ba, yana mai cewa makomar Najeriya na bukatar hadin kan kowa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.
Gumi ya yi martani ga Ministan tsaro
A baya, mun wallafa cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce babu wani lokaci da ya taɓa goyon bayan ’yan bindiga, yana mai cewa addini bai yarda da zalunci ba.
Ya yaba wa sabon ministan tsaro Janar CG Musa mai ritaya kan matsayinsa na cewa ba zai yi sasanci da miyagun ’yan bindiga da ke kashe bayin Allah ba.
Malamin ya ce ya nemi a yi wa Nnamdi Kanu afuwa ne idan zai tuba, kamar yadda aka kafa sharadi na karɓar afuwar Chukwu Ojukwu da ’yan Neja Delta a baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

