NNPP da Manyan Jam'iyyu 2 da ba a Ga Tambarinsu a Takardar Zaben Cike Gurbin Kano ba
- Hukumar zabe ta kasa (INEC) ba ta sanya jam'iyyun adawa uku, PDP, NNPP da ADC a zaben cike gurbin da ya gudana a jihar Kano ba
- Rahotanni sun nuna cewa babu tambarin ko daya daga cikin wadannan jam'iyyu a takardar kada kuri'a da aka gani a zaben da ya gudana yau Asabar
- Jam'iyyun sun zargi hukumar INEC da take hakkinsu na shiga zabe, suna mai cewa sun mika sunayen yan takararsu a hukumance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa babu tambarin manyan jam'iyyun adawa uku a takardun kada kuri'a na zaben cike gurbin yan Majalisu biyu a Kano.
A yau Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2026, Hukumar Zabe Ta Kasa, watau INEC ta gudanar da zabukan cike gurbi a karamar hukumar Ungogo da karamar hukumar Birni.

Kara karanta wannan
Ramadan: INEC ta hango abubuwa 2 da suka hana jama'a fitowa zaben cike gurbi a Kano

Source: Facebook
Jam'iyyun adawa 3 da babu a zaben Kano
Tashar Channels tv ta tattaro cewa manyan jam'iyyun adawa da ba a gani a takardar kada kuri'a ba sun hada da PDP, NNPP da kuma jam'iyyar hadaka watau ADC.
Legit Hausa ta fahimci cewa an shirya zaben ne domin cike kujeru biyu da suka zama babu kowa a Majalisar Dokokin Jihar Kano, sakamakon rasuwar ’yan majalisar da suka wakilci mazabun Kano Municipal da Ungogo a bara.
A wani taron manema labarai da aka gudanar kwanan nan, Kwamishinan Zaɓe na INEC a Kano, Abdul Zango, ya tabbatar da cewa duk jam’iyyu sun samu damar tsayar da ’yan takara, yana mai cewa hukumar ta shirya gudanar da zaɓe mai gaskiya da sahihanci.
Jam'iyyu 9 da suka fafata a zaben cike gurbi
Sai dai jerin sunayen ’yan takarar ƙarshe da INEC ta fitar ya nuna cewa jam’iyyu tara ne kawai aka tantance su, kuma babu PDP, NNPP da ADC a ciki.
Jam’iyyun da aka amince su shiga zaɓen sun haɗa da: Accord, ADP, APP, AAC, APC, APM, PRP, YPP, da jam'iyyar ZLP.
Duk da cewa INEC ba ta yi cikakken bayani kan dalilin cire manyan jam’iyyun ba,, jam’iyyun da abin ya shafa sun zargi hukumar da hana su amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki.
Zarge-zarge daga jam’iyyun da aka cire
A bangaren NNPP, wadda ke fama da rikice-rikicen cikin gida a Kano, an ruwaito cewa ɓangarori uku sun miƙa sunayen ’yan takara har guda shida a mazabun biyu, cewar Punch.
Sanata Mushud El-Jibril Doguwa, daga ɓangaren Boniface a NNPP, ya ce sun miƙa sunayen ’yan takararsu yadda ya kamata, amma INEC ta ƙi amincewa da jam’iyyar su ba tare da hujja ba.

Source: Facebook
A nasa ɓangaren, Shugaban PDP na Kano, Alhaji Yusuf Kibiya, ya zargi INEC da karya tanade-tanaden Dokar Zaɓe, yana mai cewa an ba su kwanaki huɗu kacal domin gudanar da zaɓen fidda gwani da miƙa sunayen ’yan takara.
Dalilin karancin masu kada kuri'a a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar INEC ta danganta matsalar rashin fitowar jama'a a zaben Kano da lokacin azumin watan Ramadan da kumaNkarancin jam'iyyun da suka shiga takara.
Kwamishinan Zaɓe na Jiha (REC) na INEC a Jihar Kano, Abdu Zango, ne ya bayyana hakan yayin da hira da yan jarida lokacin da ya fita duba yadda zaben ke gudana.
A cewarsa, lokacin da aka gudanar da zaɓen na iya taka rawa wajen rage yawan masu kaɗa ƙuri’a, musamman ganin cewa ana cikin watan Ramadan.
Asali: Legit.ng

