Zaben Abuja: ADC Ta Gwada Farin Jini, Ta Doke Jam'iyyar APC Mai Mulki
- Jam’iyyar hamayya ta ADC ta doke APC a rumfar zaɓe ta farko a zaɓen ƙananan hukumomi na babban birnin tarayya
- ADC ta ba wa jam'iyya mai mulki ta APC kashi a rumfa ta 076, Sani Abacha Estate, Wuse Zone 4 yayin da ta bar APC a baya
- Ɗan takarar AMAC, Dr. Moses Paul, ya yi zargin an kawo barazanar ƙoƙarin sayen kuri'a a zaɓen cike gurbin na yau
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja - Jam'iyyar ADC ta samu gagarumar nasara a rumfar zaɓe ta 076 da ke Sani Abacha Estate a Wuse Zone 4, yayin da ake ci gaba da zaɓen ƙananan hukumomi a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wannan shi ne karo na farko da jam’iyyar ta samu rinjaye a wata rumfa a zaɓen da ake gudanarwa na cike gurbi a yankin.

Kara karanta wannan
Dokar zabe: Jam'iyyar ADC ta taso Tinubu a gaba, ta fadi shirin da take yi don hana magudi

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sakamakon da aka bayyana a wurin zaɓen, ADC ta samu ƙuri’u bakwai cikin 10 da aka kaɗa.
Zaben Abuja: ADC ta lallasa APC a wata rumfa
Rahoton ya ce jam'iyyar APC ta samu biyu, ɗaya kuma aka soke shi a matsayin mara inganci da aka kada da sunan jam'iyyar.
Rumfar na daga cikin yankin birnin Abuja (AMAC), inda ɗan takarar ADC, Dr. Moses Paul, ya kaɗa ƙuri’arsa.
Zaɓen ya fuskanci ƙarancin fitowar masu zaɓe a wurare da dama. Dr. Paul ya bayyana cewa adadin mutanen da suka fito bai kai yadda aka zata ba.

Source: Facebook
Dan takarar ya danganta hakan da takunkumin zirga-zirga da aka ayyana kafin zaɓen. A cewarsa, matakin ya haddasa ruɗani tare da sanya wasu mazauna yankin kasa fitowa domin kaɗa ƙuri’arsu.
Ya ce ya shafe kusan shekaru 40 yana zaune a AMAC, amma bai taɓa ganin irin wannan yanayi ba, wanda ya kwatanta da yanayin dokar ta-ɓaci.
Duk da haka, ya yaba da yadda jami’an zaɓe suka gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da bin ƙa’ida a rumfarsa.
Ana zargin ana sayen kuri'a a zaben Abuja
'Dan takarar ya yi zargin cewa wakilan jam’iyyarsa a wasu sassa kamar Takum Shara da Kabusa Ward, ciki har da Dogongada da Shereti, sun fuskanci barazana da tsoratarwa.
Ya ce an yi masu gargaɗin cewa za a cutar da su, lamarin da ya ce yana da nufin dakile masu zaɓe tare da karkatar da sakamako.
Haka kuma ya yi ikirarin cewa ana sayen ƙuri’u a wasu sassan babban birnin, yana mai jaddada cewa hakan laifi ne a ƙarƙashin dokar zaɓe.
Duk da ƙalubalen, Dr. Paul ya nuna kwarin gwiwa cewa muradin al’umma ne zai yi nasara a ƙarshen kafa kuri'a a wannan rana.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙinsu na zaɓe, tare da ƙin amincewa da duk wata barazana ko matsin lamba daga kowace ɓangare.
Jigon ADC ya magantu kan ICPC

Kara karanta wannan
"Ana buƙatar taimako": Shehu Sani ya yi maraba da girke sojojin Amurka a Najeriya
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC har yanzu lamarin da ke yinwa manyan ADC zafi.
Wani kusa a jam'iyyar ADC, Usman Austin, ya fito ya yi magana kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan da ICPC ta ke yi bayan ta karbe shi daga hannun hukumar EFCC.
Ya shawarci ICPC da ta yi da hukumar DSS wadda ta kai karar El-Rufai gaban kotu kan wasu zarge-zarge da take yi masa a maimakon a ci gaba da tsare shi a hannunta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
