Ramadan: INEC Ta Hango Abubuwa 2 da Suka Hana Jama'a Fitowa Zaben Cike Gurbi a Kano

Ramadan: INEC Ta Hango Abubuwa 2 da Suka Hana Jama'a Fitowa Zaben Cike Gurbi a Kano

  • An samu karancin fitowar masu kada kuri'a a zaben cike gurbin 'yan majalisar dokokin Kano guda biyu a yau Asabar 21 ga Fubrairu 2026
  • Kwamishinan zabe na Kano (REC), Abdu Zango ya danganta matsalar da lokacin azumin Ramadan da kuma karancin 'yan takara a zaben
  • Ya kuma bayyana cewa duk da mutane ba su fito ba, amma zaben ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali a Ungogo da birnin Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - A yau Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026 hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke gudanar da zabukan cike gurbi na 'yan Majalisu biyu a Kano.

Sai dai rahotanni daga Kano sun nuna cewa babbar matsalar da ake fuskanta bayan fara kada kuri'a a mazabun Ungogo da karamar hukumar birni (Kano Municipal) ita ce rashin fitowar jama'a.

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: 'Yan bindiga sun sake tafka ta'addanci ana cikin azumi a Zamfara

Wurin zabe.
Yadda mutane suka fito a wata mazaba a karamar hukumar Ungogo Hoto: Muhammad T. Abubakar
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa mutane sun kaurace wa zaben cike gurbin 'yan Majalisar dokoki biyu a Kano, lamarin da ya sa aka ga jami'an INEC zaune a rumfunan zabe babu masu kada kuri'a.

Me ya jawo rashin fitowar jama'a a Kano?

Hukumar INEC ta danganta matsalar rashin fitowar jama'a da lokacin da aka shirya zaben watau cikin watan azumin Ramadan da kuma karancin jam'iyyun da suka shiga takara.

Kwamishinan Zaɓe na Jiha (REC) na INEC a Jihar Kano, Abdu Zango, ne ya bayyana hakan yayin da hira da yan jarida lokacin da ya fita duba yadda zaben ke gudana yau Asabar.

Ya ce duk da cewa an samu ƙarancin fitowar jama’a a wurare da dama, zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Tasirin azumin watan Ramadan

A cewarsa, lokacin da aka gudanar da zaɓen na iya taka rawa wajen rage yawan masu kaɗa ƙuri’a, musamman ganin cewa ana cikin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Yadda zabe ke gudana a Kano da wasu sassan Najeriya a yau Asabar

“Da farko, ina ganin lokaci ne, watakila saboda Ramadan. Na biyu kuma, akwai tunanin cewa wannan ƙaramin zaɓe ne wadda ya shafi ’yan takara kaɗan da jam’iyyu kaɗan. Ina ganin kusan ’yan takara tara ne,” in ji shi.
Zaben Kano.
Wata rumfar zabe babu masu kada kuri'a zaben cike gurbin Kano Hoto: Umar Ahmad
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa duk da ƙarancin masu kada kuri'a, an gudanar da zaɓen cikin yanayi mai natsuwa, ba tare da rahoton tashin hankali ko barazanar tsaro ba.

Zango ya yaba wa al’ummar Kano bisa halayen kirki da suka nuna yayin zaɓen, inda ya kara da cewa:

“Ta fuskar tsaro, za ku iya gani da kanku, babu wata matsala. Wannan ba irin abin da aka saba gani ba ne a Kano. Muna matuƙar yaba wa jam'a saboda yadda suka nuna ɗabi’a mai kyau. Babu tashin hankali, babu wata barazana a fili ko a ɓoye,” in ji shi.

An takaita zirga-zirga saboda zabe a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta sanar da takaita zirga-zirga a kananan hukumomin Birni da Ungogo yayin zaben cike gibi a jihar Kano.

Wannan mataki ya biyo bayan taron kwamitin shawarwari na hukumomin tsaro a lokacin zabe (ICCES), wanda Kwamishinan INEC a Kano, Zango Abdu, ya jagoranta.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar, rundunar ta sanar da cewa ta takaita zirga-zirga ne domin tabbatar da tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262