Bambance Bambance 7 da ke tsakanin Sabuwa da Tsohuwar Dokar Zaɓe

Bambance Bambance 7 da ke tsakanin Sabuwa da Tsohuwar Dokar Zaɓe

A ranar 17 ga Fabrairu, 2026, Majalisar Tarayyar kasa ta amince da sabuwar dokar zaɓe da ta kawo muhimman sauye-sauye a tsarin zaɓen Najeriya.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sabuwar dokar ta shafi batutuwa da dama da suka haɗa da kuɗin zaɓe, takardun rajista, watsa sakamakon zaɓe da kuma tsarin fitar da ’yan takara.

An amince da dokar zaben ne bayan an shafe tsawon lokaci majalisun tarayya suna aiki a kanta gabanin zabe mai zuwa.

An sanya a kan dokar zaben da ke ci gaba da tayar da kura a siyasar Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da manyan jami'an gwamnati yayin sanya hannu a kan dokar zabe Hoto; Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

BBC ta wallafa cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan dokar a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026.

Lamarin ya jawo zazzafar muharawa musamman daga jam'iyyun adawa da wadansu kungiyoyi da ke sanya ido a kan harkokin zabe saboda abubuwan da sabuwar dokar ta kunsa.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Jam'iyyar ADC ta taso Tinubu a gaba, ta fadi shirin da take yi don hana magudi

A wani sako da Renewed hope ta wallafa a shafin Facebook, ana iya ganin manyan sauye-sauyen da dokar ta zo da su.

Muhimman sauye-sauyen 7 cikin dokar zabe ta 2026:

1. Lokacin sakin kuɗin zaɓe

Kafin sabuwar dokar da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu, ana sakin kudin zabe ne akalla watanni 12, wato shekara guda kenan kafin zabe.

Amma a sabuwar dokar, za a rika sakin kuɗin zaɓe ga hukumar zaɓe ta 'kasa (INEC) aƙalla watanni 6 kafin gudanar da babban zaɓe.

2. Takardun rajistar zaɓe

A tsohuwar dokar zabe, ana amfani da katin shaidar dan kasa, wato NIN, lasisin tuki, takardar haihuwa da fasfon kasa wajen yi wa jama'a katin zaben.

Amma a sabuwar dokar, za a rika amfani da NIN, katin dan kasa da takardar haihuwa wajen yi wa yan kasa rajistar katin zaben.

3. Saukar da katin zaɓe ta yanar gizo

A baya, hukumar zaben ba ta bayar da damar saukar da katin zaɓe ta yanar gizo ba, sai dai a karɓa kai tsaye daga ofisoshin INEC da aka tanada.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke tsohon hadimin Buhari yayin da El Rufa'i ke tsare

Amma a sabuwar dokiar zaben, 'yan kasa da suka yi rajista za su iya saukar da katin zaɓensu kai tsaye daga shafin yanar gizon INEC.

4. Lokacin miƙa sunayen ’yan takara

A baya ana buƙatar miƙa sunayen 'yan takara ga hukumar INEC kwanaki 180 kafin zaɓe, amma a sabuwar dokar da Tinubu ya sanya wa hannu a rage kwanakin.

A yanzu, dole ne jam’iyyun siyasa su miƙa sunayen ’yan takararsu kwanaki 120 kafin ranar zaɓe.

5. Fitar da jerin ’yan takara daga INEC

A baya, hukumar zabe ta kasa, INEC na wallafa jerin sunayen 'yan takara ne kwanaki 150 kafin lokacin zaɓe.

Amma a sabuwar dokar, dole ne hukumar INEC ta rika wallafa jerin ’yan takara kwanaki 60 kafin ranar zaɓe.

6. Watsa sakamakon zaɓe ta IReV

A baya, babu wani sashe na dokar zabe da ya fayyace wajibcin tura sakamakon zabe kai tsaye ta na'ura ba, amma a sabuwar dokar, an yi wannan tanadi.

A yanzu, aika sakamakon zaɓe zuwa manhajar IReV ya zama dole. Amma idan aka samu matsala, ana iya amfani da takardar sakamakon zabe ta EC8A domin hada sakamakon.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Shugaba Tinubu ya fadi dalilin sanya hannu a dokar zabe duk da korafe korafe

7. Tsarin zaɓen fitar da gwani a jam’iyyu

A baya ana amincewa da zaɓen fitar da gwani ta hanyar ba wakilan jam'iyya wato 'delegates' su zabi dan takara, amma an cire shi daga sabuwar doka.

Yanzu an amince da tsarin zaɓen fitar gwani na kato-bayan-kato, wanda zai ba 'yan jam'iyya damar su fito su zabi wanda suke so da tsarin maslaha kaɗai.

Wadannan sauye-sauye, musamman bangaren aika sakamakon zabe ta hanyar intanet inda aka sassauta zuwa amfani da fam da INEC za ta samar na ci gaba da tayar da kura a siyasa.

Dokar zabe: Kwankwasiyya ta kalubalancI Tinubu

A baya, mun wallafa cewa kungiyar Kwankwasiyya ta soki sahalewar gaggawa da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi wa sabuwar dokar zaben kasar nan.

Kungiyar ta ce karfin APC a majalisa da yawaitar sauya sheka na barazana ga daidaito da tsarin dimokuradiyya, wanda ba zai taba haifiar da 'da mai ido ga ci gaban Najeriya ba.

Kwankwasiyya ta gargadi ‘yan siyasa su rika tuna amanar wadanda suka zabe su, tare da kira ga jama’a su tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin dimokuradiyya Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng