Yadda Zabe ke Gudana a Kano da Wasu Sassan Najeriya a Yau Asabar
- A yau Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026 ake gudanar da zaben cike gibi a wasu jihohin Najeriya da suka hada da Kano da Rivers
- A birnin tarayya Abuja, ana gudanar da zaben kananan hukumomi, inda jama'a suka fara tafiya zuwa rumfunan kada kuri'a tun da safe
- A wannan labarin, Legit ta tattaro muku halin da aka shiga tun daga sanyin safiyar yau zuwa daidai lokacin hada wannan rahoton
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tun da sanyin safiyar yau Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026 jami'an hukumar INEC suka fara isa rumfunan zabe a Kano, Abuja da Rivers.
A jihohin Kano da Rivers, za a gudanar da zaben cike gibi na kujerun 'yan majalisa yayin da za a yi zaben kananan hukumomi a birnin tarayya Abuja.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro muku abubuwan da ke cigaba da faruwa a wasu daga cikin rumfunan zabe a yankunan da ake zaben.
Yadda zabe ke gudana a Kano
Wasu rahotanni sun nuna cewa an samu karancin masu kada kuri'a yayin da ake zabe a karamar hukumar Birni da Ungogo a Kano.
Premier Radio ya wallafa a Facebook cewa ma’aikatan zabe da jami’an tsaro sun fita bakin aiki da wuri amma babu al’umma masu zabe sosai.
Wasu rahotanni sun yi zargin cewa babu jam'iyyar NNPP da Sanata Rabiu Kwankwaso ke jagoranta a takardar kada kuri'a, sai dai har yanzu babu cikakken bayanin hukuma game da hakan.
Tsohon shugaban karamar hukumar Ungogo, Sani Abdu ya yi bayani game da yadda zaben ke tafiya a wani bidiyo da Musayyib Kawu ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce:
"Ba a samu tangarda ba, kuma jami'an INEC na yin abin da ya kamata."
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu labarin tashin hankali tsakanin jam'iyyu ko 'yan daba ba, sai dai ba a san me zai biyo baya ba.
Yadda zabe ke tafiya a birnin Abuja
Kamar jihar Kano, jaridar Punch ta wallafa cewa an samu karancin masu kada kuri'a a wasu sassan Abuja kamar AMAC da sauransu.
Shafin ADC Vanguard ya wallafa a X cewa jami'an INEC sun isa mazabar Nuku/Sabon Gari da ke Abaji da misalin karfe 7:46 na safe, sai dai an samu sabani tsakaninsu da wakilan jam'iyyar.
Ita kuwa Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa masu abubuwan hawa da suka hada da 'yan acaba sun ki bin umarnin zama a gida sun fita sun cigaba da harkokinsu.

Source: Facebook
Hukumar INEC ta wallafa yadda masu kada kuri'a suka isa rumfunan zabe a shafinta a Facebook, tare da yadda aka ba masu bukata ta musamman damar kada kuri'a.
Yadda zabe ke tafiya a yankunan Rivers
Rahoton Channels TV ya nuna cewa na samu karancin masu kada kuri'a kamar yadda lamarin ya ke a jihar Kano da Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa an cire jam'iyyun PDP da ADC daga cikin masu neman kujerun da ake nema a Ahoada da Khana.
The Nation ta rahoto cewa bisa jerin sunayen ’yan takarar da hukumar INEC ta fitar domin zaɓen, jam’iyyar PDP da ADC ba su cikin takardar kaɗa ƙuri’a.
An takaita zirga zirga a Kano
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta sanar da takaita zirga-zirga a yankunan karamar hukumar Birni da Ungogo.
Kwamitin tsaro mai lura da zabe na jihar Kano ya tattauna da masu ruwa da tsaki game da matakan da ya ce zai dauka a yau Asabar.
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Bakori ya bayyana cewa za su tattabar da komai ya tafi lafiya yayin da ake gudanar da zaben.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


