‘Abin da Zai Sa na Iya Yin Rawa a Yanzu’: Pantami Ya Magantu kan Tsunduma Siyasa

‘Abin da Zai Sa na Iya Yin Rawa a Yanzu’: Pantami Ya Magantu kan Tsunduma Siyasa

  • Farfesa Isa Ali Pantami ya yi karin haske kan dalilin da ya sa yake shiga harkokin siyasa, yana mai cewa akwai abin da mutane ba su fahimta
  • Tsohon ministan ya musanta zargin cewa zai yi rawa a siyasa, yana cewa ko a lokacin da yake rike da kujerar minista bai taba aikata hakan ba
  • Pantami ya ce zai iya yin duk wani abu domin maslahar al’umma, har ma ya ce idan hakan zai ceci rayuka, zai iya rawa ko ba don mulki ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi maganganu game da dalilan shigarsa siyasa a yanzu.

Sheikh Isa Pantami ya yi magana kan batutuwa da suka shafi yadda ake sukarsa da kuma abin da yake ganin mutane suka jahilta game da siyasa.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Pantami ya wanke kansa kan batun haramta wa malamai shiga siyasa a baya

Pantami ya fayyace komai game da shigarsa siyasa
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Source: Twitter

Pantami ya soki masu ihun ya shiga siyasa

Pantami ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da BBC Hausa wanda aka wallafa a shafin Facebook a yau Asabar 21 ga watan Fabrairun 2026.

A cikin bidiyon, Pantami ya tabo batun suka da yake sha game da cewa zai yi rawa a siyasa inda ya soki masu magana bayan wani dan jarida ya kalubalance shi.

Malamin ya ce akwai rashin fahimta da wasu ke da shi na addini da rayuwa inda ya ce ko a lokacin da yake minista bai yi rawa ba.

Ya ce:

"Rashin fahimtar addini mai zurfi da rayuwa mai zurfi yana ruda wasu, farko abin zan fada maka shi ne yanzu ba na yi minista ba, da nake minista duk abin da ya ce zan yi na taba yi?.
"Da ni aka yi babban taron jam'iyya, na ta shi na yi? ranar da shugaban kasa ya zo kamfen takara Gombe ina kan durom din siyasa na yi magana, a Fabraitun 2023 na yi rawa?"

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya fadi dalilin shiga siyasa da neman gwamna a Gombe

Pantami ya fadi dalilin da zai sa ya yi rawa
Tsohon minista a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Sheikh Pantami ya ja hankalin al'umma

Sheikh Pantami ya tunatar da mutane wasu matsaloli da ka iya tasowa da mutum zai kauce hanya domin kawo maslaha da al'umma.

Ya ce zai iya taka rawa ko da kuwa bai cikin siyasa tsundum saboda dakile wata matsala musamman domin ceto rayuwar wasu al'umma.

"Me yasa za mu duba dukkan harkan shugabanci, duk maganar da ke ci wa mutane ba za mu magance ta ba, sai wata matsala ko barna kwaya daya a ciki.
"Duk wanda ya san addini, ya san akwai abubuwa haka, ba sai ina siyasa ba, idan misali aka ce za a kai hari a Najeriya, sai maharan suka ce ba za su sake su ba sai Isa Ali ya yi rawa, idan dai rawar da zan yi zai sa a sake su, wallahi zan yi."

- Farfesa Isa Ali Pantami

Pantami ya fusata da ake yi masa sharri

Kara karanta wannan

Sheikh Bashir Aliyu ya yi wa Tinubu raddi kan rokon 'yan Najeriya su yafe masa

A baya, an ji cewa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya fusata kan wasu zarge-zarge da ake yadawa kansa game da zargin tsattsauran ra'ayi a baya.

Malamin ya karyata zargin kisan kai baki ɗaya, yana cewa ba ya da hannu kai tsaye ko a kaikaice inda ya gargadi masu yada hakan.

Ya nemi bayanan masu zargi domin daukar matakin shari’a, yana mai bayyana dogaro da bayanan AI kamar Grok a matsayin kuskure.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.