Sheikh Pantami Ya Fadi Dalilin Shiga Siyasa da Neman Gwamna a Gombe

Sheikh Pantami Ya Fadi Dalilin Shiga Siyasa da Neman Gwamna a Gombe

  • Tsohon ministan sadarwa na Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi karin bayani geme da shigarsa siyasa dumu-dumu da neman gwamna
  • Malamin ya bayyana yadda ya je dakin Ka'aba yana rokon Allah ya datar da shi game da rokon da aka masa ya tsaya takarar gwamna a Gombe
  • Pantami ya yi bayanin ne yayin da 'yan siyasa daga jam'iyyu da dama suka fara shiri domin tunkarar zaben shekarar 2027 da za a yi a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana dalilin shiga siyasa tare da niyyar neman gwamnan jihar Gombe a zaben shekarar 2027.

Tsohon ministan ya fadi abubuwan da zai mayar da hankali a kansu wajen kawo cigaba a jihar Gombe idan Allah ya ba shi nasara a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan kashe kashe a taron APC, ya dauki kwakkwaran mataki

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami yayin wa'azi a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Sheikh Pantami ya bayyana haka ne a wata hira da tashar BBC Hausa yayin da aka fara shirin tunkarar siyasar shekarar 2027 a Najeriya.

Dalilin shigar Pantami siyasa

Sheikh Pantami ya ce manyan malamai a ciki da wajen Najeriya da ma manyan magabata na kiran mutane masu nagarta su shiga siyasa.

Ya bayyana cewa yana da maganganun Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Sheikh Dahiru Bauchi, Dr Bashir Aliyu Umar da Dr Sani Umar Rijiyar Lemo kan cewa ya kamata mutanen kirki su shiga siyasa.

Me yasa Pantami takarar gwamna?

Dangane maganganun da ake cewa malamin na shirin tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe, Pantami ya yi yikarin bayani kan hakikanin abin da ke faruwa:

Pantami ya ce:

''Akwai 'yan'uwa da dama waɗanda tun da na bar ofishin ministan sadarwa, bayan ganin ɗimbin ayyukan alkairan da na kai wa jihar Gombe na sama wa yara ayyukan yi da horas da mata da bayar da tallafi da sauransu''.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

‘'Su ne suka ga dacewar tsayawata takarar gwamnan jihar Gombe, inda suka riƙa tururuwar na zo na shiga na tsaya takarar gwamnan,''

Malamin ya bayyana yadda ya roki Allah a dakin Ka'aba ya yi addu'a, ya ce:

''Har istikara a ɗakin ka'aba sai da na yi domin neman zaɓin Allah, sai na ji ƙiyayyar da nake yi wa takarar tana raguwa, har daga baya na zo na ji na gamsu,''
Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami a ofishin APC a Gombe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Aikin da Pantami zai yi a Gombe

Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa idan Allah ya ba shi damar zama gwamnan a Gombe, zai ɗaura a kan abin da gwamna jihar na yanzu ke yi.

Pantami ya ce:

''Babban abin da za mu mayar da hankali a kai shi ne samar da ayyukan gina al'umma da kafa masana'antu, janyo masu zuba jari daga ƙetare.''

Ga bidiyon hirar Pantami a kasa:

Kiran sakataren APC ga Pantami

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon minista, Sheikh Isa Ali Pantami ya ziyarci ofishin APC domin sabunta katin jam'iyya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Izala ta dakatar da tafsiri, ta kira taron gaggawa a Kaduna

Sakataren tsare-tsaren APC na jihar, Ibrahim Bakas ya bayyana cewa malamin ya ba su gudumawa sosai a rajistar da suka yi.

Duk da haka, Ibrahim Bakas ya bayyana cewa dole Sheikh Pantami ya tika rawa, domin gwamnan jihar na yanzu ma ya yi rawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng