Bayan Kanannaɗe El Rufai, Ana Zargin Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Cafke Tsohon Gwamna

Bayan Kanannaɗe El Rufai, Ana Zargin Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Cafke Tsohon Gwamna

  • Jam’iyyar ADC ta bankado wani shiri da take zargin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta shirya cafke tsohon gwamnan Rivers
  • ADC ta tabbatar da cewa ana shirin cafke jigonta a jihar da Najeriya, Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi ba tare da dalili ba
  • Hakan na zuwa ne bayan cafke tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da ake ganin bita da kullin siyasa ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Jam’iyyar ADC a Jihar Rivers ta tabbatar da cewa akwai wani shiri na cafke jigonta kuma tsohon gwamnan Rivers.

ADC tana zargin gwamnatin Bola Tinubu na shirin cafke tsohon ministan sufuri, Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi.

Ana zargin gwamnatin Tinubu za ta cafke Amaechi
Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Source: Twitter

Sakataren yada labarai na ADC a jihar, Cif Luckyman Egila, ne ya bayyana hakanyayin wata tattaunawa da jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Yadda ake ci gaba da tsare El-Rufai

Hakan na zuwa ne bayan hukumomi a Najeriya ke ci gaba da tsare tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai bayan ya kai kansa ofishin EFCC da suka gayyace shi.

El-Rufai ya je ofishin ne kwana ɗaya bayan jami'an sun tare shi a filin jirgin saman Abuja jim kadan bayan ya dawo daga ketare.

Zargin da ADC ke yiwa gwamnatin Tinubu

Egila ya ce a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa a ƙasar, ADC da manyan jagororinta sun zama abin da kullum gwamnati ke kai masu hari.

Ya tuna cewa an taba cafke El-Rufai ta hannun DSS, yana mai cewa hukumomi na bibiyar duk wanda suke gani a matsayin dan adawa.

Ya ce:

“Za ka iya kiransa jita-jita, amma siyasa ce kuma ba za mu iya watsi da shi gaba ɗaya ba.
“A halin yanzu a Najeriya, ADC ce babbar jam’iyyar adawa da ke kokarin kayar da jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fusata da rigimar APC ta lakume rayukan mutane 2, ya ba da umarni

“Ba za mu ce babu wani shiri ba, domin suna kokarin cafke duk wanda zai iya kalubalantar ko kayar da su.”

- Luckyman Egila

ADC ta zargin ana shirin cafke Amaechi
Tsohon minista a mulkin Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Source: Twitter

Abin da ADC ke yi a halin yanzu

Egila ya ce a yanzu sun saka ido ta ko ina domin tabbatar da kare lafiyarsa inda ya ce suna fatan ba za su kai ga nasarar cafke shi ba kamar yadda suke zargi.

Egila ya ce:

“A yanzu muna sa ido. Muna fatan ba za su kai ga wannan mataki ba, domin ‘yan Najeriya ma na sa ido.”

Ya kara da cewa ADC jam’iyya ce mai bin doka, kuma har yanzu ba su samu wani bayani a hukumance kan yiwuwar cafke Amaechi ba.

Za a kai Nasir El-Rufai kotu

Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Hukumar DSS ta sanya lokacin gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu kan wasu zarge-zarge da take yi masa.

DSS ta gabatar da tuhume-tuhume uku a gaban kotu kan El-Rufai bisa zarge-zargen da ke alaka da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.