Ana Shirin Zabe a Abuja, 'Yan Takara 2 Sun Janye, Sun Marawa Jam'iyyar APC baya
- Julius Adamu na jam'iyyar PDP ya janye wa dan takarar APC a karamar hukumar Bwari bayan shiga tsakani da ministan Abuja
- Godson Nemieboka na jam'iyyar AA shima ya janye wa Christopher Zakka na APC a AMAC domin gujewa rarrabuwar kawuna
- Hukumar zabe ta INEC ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomin babban birnin tarayya Abuja a ranar Asabar mai zuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Bwari a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Julius Adamu, ya janye daga takara domin marawa ɗan takarar APC, Joshua Musa baya.
Adamu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan tattaunawa da ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, inda ya ce su biyun ƴan uwan juna ne.

Source: Twitter
Dan takarar PDP ya marawa APC baya

Kara karanta wannan
'Yan daba sun fasa ofishin APC, sun raunata shugaban jam'iyya, tsohon dan majalisa
Wike ya buƙaci mazauna Bwari da su zaɓi ɗan takarar na APC, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin hanyoyi idan har jam'iyyar ta yi nasara, cewar rahoton Channels TV.
Ministan ya jaddada cewa haɗin kan ƴan takarar zai kawo ci gaba mai ɗorewa ga yankin na Bwari a cikin ƙanƙanin lokaci yanzu.
Julius Adamu ya ce:
"Yau gani gabanku, don in sanar da ku cewa bayan tattaunawa mai zurfi da ministan Abuja, Nyesom Wike, na fahimci cewa ni da Joshua duk 'yan uwan juna ne.
"Bai kamata a ga 'yan uwa suna fada a kan kujera daya ba. Don haka, na marawa Hon. Joshua baya. Ina kiran daukacin magoya bayana da su zabi Joshua don ya yi nasara a zaben nan."
Dan takarar AA ya koma bayan APC
Haka kuma, ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar kwaryar birnin Abuja (AMAC) a jam’iyyar AA, Godson Nemieboka, ya janye daga zaɓen da za a gudanar.
Nemieboka ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar APC mai ci, Christopher Zakka, kasa da sa'o'i 48 kafin a fara jefa ƙuri'a, in ji rahoton Leadership.
Godson Nemieboka ya bayyana cewa:
"Ban yanke wannan shawarar cikin gaggawa ko matsin lamba ba. Na dauki wannan matakin ne don guje wa rarrabuwar kawuna a siyasar yankinmu."
Ya ƙara da cewa dukkan dabarun yaƙin neman zaɓensa da magoya bayansa yanzu za su koma aiki ne domin ganin jam'iyyar APC ta yi nasara a ranar Asabar.

Source: Twitter
APC na samun karfi a Abuja
Ya yi kira ga magoya bayansa da su kasance cikin zaman lafiya da tsari yayin da ake tunkarar wannan babban zaɓe na manyan biranen ƙasar nan.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) tana ci gaba da shirin gudanar da zaɓen kansiloli da shugabannin ƙananan hukumomi shida da ke faɗin babban birnin tarayya Abuja.
Waɗannan sauye-sauye na janye wa ƴan takara na nuna yadda jam'iyyar APC ke samun ƙarfi sakamakon tsoma baki da ministan birnin tarayya Nyesom Wike ya yi yanzu.
Tsohon shugaban AMAC ya koma APC
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban ƙaramar hukumar kwaryar birnin Abuja (AMAC), Prince Nicholas Ukachukwu ya sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da batun El Rufai, an fara yunkurin soke rijistar jam'iyyar ADC da jam'iyyu 4 a Najeriya
Ukachukwu ya kuma bayyana cewa ya amince da kiraye-kirayen da ake masa na tsayawa takarar gwamnan jihar Anambra a zaɓen jihar da za a yi.
Tsohon shugaban karamar hukumar ya ce idan mutane suka zaɓe shi ya hau kan karagar mulki, zai magance matsalar tsaro, talauci da sauransu cikin watanni uku kaɗai.
Asali: Legit.ng
