Tambuwal Ya Harzuƙa, Ya Faɗi Yadda Ƴan APC Suka 'Fi Karfinsu' kan Dokar Zaɓe
- Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya zargi shugabancin majalisa da gaggauta amincewa da muhimmin sashe na dokar zaɓe
- Aminu Waziri Tambuwal ya yi gargadin cewa hakan na iya buɗe ƙofa ga magudi ganin cewa jam'iyya mai mulki na amfani da karfinta
- Yana wannan batu ne bayan majalisa ta amince da sabuwar dokar zaɓe duk da adawar da sauran jam'iyyu ke yi da sashen aika sakamakon zaɓe
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon gwamnan Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal ya dauki batun dokar zaɓe da zafi.
Sanatan ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda shugabannin Majalisar Dattawa suka tafiyar da muhimmin sashe na gyaran dokar zaɓe.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Tambuwal ya ce an yi amfani da ƙarfin iko wajen tabbatar da cewa an amince da wani sashe na kudirin.
Yadda aka nuna adawa a dokar zaɓe - Tambuwal
Daily Post ta ruwaito cewa duk da ɓangaren marasa rinjaye sun nuna ƙin amincewa da wani sashe na dokar zaɓe, ƴan adawa sun yi gaban kansu.
Ya kara da cewa rikici ya ɓarke ne a zauren majalisa bayan da aka ƙi sauraron bukatar ‘yan adawa na a dakata, a sake duba sashen domin a samu daidaito kafin a kada kuri’a.
Tambuwal ya ce a farkon batun, abin da aka gabatar shi ne sauya wa’adin da hukumar zaɓe ke bayar da sanarwa daga kwanaki 360 zuwa 300.
A cewarsa, an kawo wannan shawara ne domin a daidaita jadawalin zaɓe da watan azumin Ramadan na shekara mai zuwa.
Tambuwal ya zargi yan APC da karfa-karfa
Sai dai Aminu Waziri Tambuwal ya ce abin ya sauya salo daga batun daidaita jadawalin zabe zuwa abin da ya kira karfa-karfa.
A kalamansa:
"An matsa mana lamba aka amince da wani sashe na dokar zaɓe ba tare da a yi cikakken nazari ba.”
Ya ƙara da cewa bayanan da suka samu sun nuna cewa shugabannin majalisun biyu sun zauna, inda suka fi karkata ga ra’ayin da Majalisar Dattawa ta gabatar tun farko.

Source: UGC
Tambuwal ya ce a lokacin da aka fahimci abin da ke faruwa, sai ɓangaren su suka nuna rashin amincewa, suna mai neman a bi doka da oda ta hanyar yin kuri’a.
Ya kara da cewa hakan ne kaɗai zai tabbatar da gaskiya da adalci a tafiyar da dokoki masu muhimmanci irin wannan.
Sanatan ya kuma jaddada cewa akwai fargabar cewa wasu sauye-sauyen da ake ƙoƙarin amincewa da su za su iya haifar da wata kafa da za a yi anfani da ita wajen magudin zaɓe.
Ya ce manufar gyaran dokar ya kamata ta kasance ƙarfafa gaskiya da rage kura-kurai, ba buɗe hanyoyin da za su iya jawo shakku ba.
Tinubu ya sa hannu a kan dokar zaɓe
A baya, mun wallafa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kudurin dokar zaɓe ta shekarar 2026 bayan ya rattaba hannu a kai domin zama doka a hukumance.
Wannan ya zo ne bayan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta kammala nazari tare da amincewa da kudirin bayan watanni ana muhawara da tattaunawa kan muhimman sauye-sauyen da aka gabatar.
Sabuwar dokar ta soke dokar zaɓe ta 2022, inda aka ce an yi gyare-gyare domin ƙarfafa tsarin zaɓe da kuma magance ƙalubalen da aka fuskanta a zaɓukan baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


