Kano: Tashin Hankali a Gidan Kwankwaso, an Gano Wani Makusancinsa a Taron APC

Kano: Tashin Hankali a Gidan Kwankwaso, an Gano Wani Makusancinsa a Taron APC

  • Rikici ya ƙara tsananta a ɓangaren NNPP na Rabiu Musa Kwankwaso bayan wani na kusa da shi ya bayyana tare da jiga-jigan APC.
  • Matakin Bichi ya jefa magoya bayan Kwankwaso cikin ruɗani, tare da fargabar ƙarin sauya sheƙa a Kano.
  • Masu goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf sun yi murna, suna cewa tsarin Kwankwasiyya na rushewa a jihar.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sabon yanayi na ruɗani ya mamaye ɓangaren jam’iyyar NNPP da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta a Kano.

Hakan ya biyo bayan bayyanar Hon. Ahmad Garba Bichi tare da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a bainar jama’a.

Matsala a Kwankwasiyya bayan ganin abokin Kwankwaso a taron APC
Rabi'u Kwankwaso, Ahmad Garba Bichi da Abba Kabir. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

Legit Hausa ta samu wani faifan bidiyo da hadimin Gwamnan Kano, Ibrahim Adam ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Yadda ake kallon Bichi a Kwankwasiyya

Kara karanta wannan

Manyan jam'iyyar APC da aka gani wajen tarbar gwamna Abba daga NNPP a Kano

Bichi, wanda da dama ke kallonsa a matsayin ginshiƙi mai ƙarfi a cikin ɓangaren, an hango shi a ranar Litinin, 16 ga Fabrairun 2026, yayin wani taron maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Wannan lamari ya ƙara haddasa hasashe a siyasar Kano, inda mambobin NNPP da dama suka fara tambayar makomar ɓangaren da kuma makomar tsarin Kwankwasiyya a jihar.

Binciken wakilin Legit.ng ya nuna cewa matakin da Bichi ya ɗauka na nuna goyon baya ga sansanin gwamnan ya jefa magoya bayan Kwankwaso cikin ruɗani.

Wata majiya daga ɓangaren Kwankwaso ta bayyana cewa wannan mataki babban koma baya ne ga tsarin, tana mai cewa ba su taɓa tsammanin hakan ba.

Majiyar ta ce:

“Hon. Bichi ginshiƙi ne a gare mu. Yanzu da ya rungumi bangaren gwamna, ba mu san abin da zai biyo baya ba.”

Ta ƙara da cewa akwai fargabar cewa matakin Bichi zai iya haifar da sauya sheƙa a jere, inda wasu shugabanni ke shirin sauya sheƙa sakamakon rashin tabbas.

An maganganu kan ganin na kusa da Kwankwaso a taron APC a Kano
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

Yadda ɓangaren Gwamna ke kallon lamarin

Sai dai sababbin abokan siyasar Gwamna Yusuf a APC sun bayyana farin cikinsu kan lamarin, suna ganin hakan wata babbar nasara ce a gare su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gidan limamin masallacin Izala da dare, sun sace iyalansa

Mai ba gwamna shawara, Hon. Ibrahim Adam, ya yi iƙirarin cewa tsarin Kwankwasiyya a Kano na rushewa, yana mai cewa manyan mambobi sun koma bangaren gwamna.

Ya ce:

“Ko waɗanda ake ganin suna tare da su duk sun sauya sheƙa. Daga matakin unguwa zuwa jiha, yanzu suna tare da gwamna.”

Rikicin NNPP a Kano ya samo asali ne tun bayan sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir zuwa APC a watan Janairun 2026.

Kawu Sumaila ya tabo Ado Doguwa a Kano

Kun ji cewa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya roki jama’a su guji mayar wa Alhassan Ado Doguwa martani, yana cewa yana fuskantar wata matsala.

Sanatan ya ce wasu abubuwa da suka faru a baya ne suka taru a kansa, yana mai jaddada cewa na kusa da shi sun dade da lura da halayensa.

Kawu ya kuma gargadi magoya baya su daina tsokanar Doguwa, yana mai cewa abin da yake bukata yanzu shi ne goyon baya da addu’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.