'Ina EFCC?': Watsa wa Rarara Kudi a gaban Tinubu Ya Tayar da Kura, an Gargadi ’Yar APC

'Ina EFCC?': Watsa wa Rarara Kudi a gaban Tinubu Ya Tayar da Kura, an Gargadi ’Yar APC

  • Wata mata da ake ganin mai goyon bayan APC ce ta watsa takardun Naira yayin da mawaki Kahutu Dauda Rarara ke waka a gaban Bola Tinubu
  • Hakan ya biyo bayan ziyarar shugaban kasar a Adamawa, inda ya kaddamar da wasu muhimman ayyukan da Gwamna Ahmadu Fintiri ya yi a jihar
  • Dokar Najeriya ta haramta watsa ko cin zarafin Naira, kamar yadda Sashe na 21 na dokar CBN ya tanada, tare da hukunci ga masu karya doka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - An gargadi wata mata mai goyon bayan jam’iyyar APC bayan ta watsa kudi yayin taro a jihar Adamawa.

Matar ta yi haka ne da mawaki Dauda Kahutu Rarara, ke gabatar da waka domin karrama Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a jihar.

Kara karanta wannan

Barau ya bude kofar bada tallafi, ya mika N100m ga 'yan kasuwar Singer

Ana ce-ce-ku-ce bayan watsa wa Rarara kudi a gaban Tinubu
Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara da Bola Tinubu. Hoto: @daudakahuturarara/abat.
Source: Instagram

Lamarin ya faru ne a lokacin da shugaban kasa ya kai ziyara domin kaddamar da wasu muhimman ayyukan raya kasa da gwamnatin Ahmadu Umaru Fintiri ta aiwatar, cewar Punch.

Ayyukan da Tinubu ya kaddamar a Adamawa

Daga cikin ayyukan da aka kaddamar akwai sababbin makarantu na zamani a kananan hukumomi 21 na jihar, wadanda suka kunshi sassan firamare, sakandare, da wuraren wasanni tare da kayan koyarwa na zamani.

Haka kuma an bude wata gada mai layuka takwas a kan titin Galadima Aminu, bayan gyara babbar kotu da gina sabon zauren taro, da kuma sababbin gine-ginen ofisoshin gwamnati.

An watsa wa Rarara kudi a gaban Tinubu

Yayin da mawaki Rarara ke rera sabuwar wakarsa mai taken “Omo Ologo,” wacce ya sadaukar wa shugaban kasa, wata mata sanye da kayan APC ta matsa kusa da mawakin cikin farin ciki tare da watsa wasu takardun Naira a gabansa.

Kara karanta wannan

Gwamatin Tinubu ta gargadi matasa masu shiga soja a Rasha, ta gano yadda ake yi

Sai dai nan take aka gargade ta kan wannan dabi’a, domin dokokin Najeriya sun haramta watsa kudi ko amfani da su ta hanyar da ke bata darajarsu.

An gargadi yar APC da ta watsa wa Rarara kudi a gaban Tinubu
Mawaki Dauda Kahutu Rarara da matarsa, Aisha Humairah yayin da suka ziyarci Bola Tinubu. Hoto: Dauda Kahutu Rarara.
Source: Twitter

Abin da doka ta ce kan wulakanta kudi

Sashe na 21 na dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa duk wanda ya wulakanta ko ya lalata takardun Naira na iya fuskantar hukunci a gaban doka.

Babban Bankin Najeriya ma ya dade yana aiwatar da manufofi daban-daban domin kare inganci da mutuncin kudin kasar.

A baya-bayan nan ma, an gurfanar da wasu mutane a kotu kan zargin watsa kudi a bukukuwa, abin da ke nuna yadda hukumomi ke daukar matakin tsaurara kan cin zarafin Naira.

An kalubalanci yadda EFCC ke aikinta

Wani mai amfani da X, agbomabiwon01 ya wallafa bidiyon a shafinsa inda yake cewa abin mamaki ana watsa takardun Naira a gaban Shugaba Bola Tinubu.

Ya ce idan da a ce wani ya yi wannan kuskuren da warhaka EFCC sun hallara a wurin, ya ce shin doka kam su waye kadai ta shafa?

Albishir da Tinubu ya yiwa yan Najeriya

Kara karanta wannan

An kada hantar Kwankwaso, Barau ya yi alkawari ga Abba, Tinubu kan zaben 2027

Kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a sassa daban-daban na Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwammatinsa a shirye take wajen ganin ta yi nasara kan 'yan bindiga da 'yan ta'adda.

Tinubu ya kuma yaba wa dakarun tsaron Najeriya kan irin kokarin da suke yi wajen yaki da 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.