Ana tsaka da Batun El Rufai, An Fara Yunkurin Soke Rijistar Jam'iyyar ADC da Jam'iyyu 4 a Najeriya
- Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta fara sauraron karar da aka nemi soke rijistar jam'iyyar ADC da wasu jam'iyyu hudu a Najeriya
- A zaman da kotun ta yi ranar Litinin, 16 ga Fabrairun 2026, ta sanya ranar 24 ga watan da muke ciki domin ci gaba da sauraron karar
- Masu ƙarar sun shaida wa kotu cewa jam’iyyun ba su samu kashi 25 cikin ɗari na ƙuri’u a kowace jiha ba a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Yayin da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya fara fuskantar bincike daga hukumomin gwamnati, an fara yunkurin soke rijistar jam'iyyarsu ta hadaka, ADC.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 24 ga Fabrairu, 2026, domin sauraron wata ƙara da ke neman a tilasta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.

Source: Getty Images
Jaridar The Cable ta tattaro cewa an shigar da karar neman soke rijistar wadannan jam'iyyu ne bisa zargin sun karya kundin tsarin mulkin Najeriya.
Jam'iyyu 5 da aka nemi kotu ta soke su
Wasu mambobi daga Kungiyar Amintattun Wakilan Tsofaffin ’Yan Majalisa ne suka shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/25
Wadanda masu kara suka shigar gaban kotun sun hada da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Antoni Janar na Tarayya (AGF) da jam'iyyun ADC, Accord, ZLP, AA da APP.
An fara tsara sauraron shari’ar ne a gaban Mai Shari’a Peter Lifu a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2025 amma ba a ci gaba da shari’ar ba, lamarin da ya sa kotun ta ɗage zuwa ranar 24 ga Fabrairu.
Dalilan da masu kara suka gabatar a kotu
Masu ƙarar sun shaida wa kotu cewa jam’iyyun ba su samu kashi 25 cikin ɗari na ƙuri’u a kowace jiha ba a zaɓen shugaban ƙasa na ƙarshe da ya gabata.
Sun kuma ce jam’iyyun ba su lashe ko kujera ɗaya ba a zaɓukan cike gurbi na watan Agusta 2025 da INEC ta gudanar, wanda suka ce bai cika ƙa’idar doka ba.
Saboda haka, sun roƙi kotu ta ayyana cewa jam’iyyun sun gaza cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki da Dokar Zaɓe suka shimfiɗa, tare da umartar a soke rajistarsu.
Tanadin dokar Najeriya
Sashe na 225 na Kundin Tsarin Mulki ya bai wa INEC ikon soke rajistar duk wata jam’iyya da ta karya sharuɗɗan rajista ko ta kasa cimma mafi ƙarancin ma’aunin zaɓe, ciki har da samun aƙalla kashi 25% na ƙuri’u a kowace jiha a zaɓen shugaban ƙasa.
A watan Fabrairu 2020, INEC ta soke rajistar jam’iyyu 74 bisa gazawa wajen cika sharuɗɗan da sashe na 225(a) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya tanada.
Daga bisani, a watan Maris 2022, kotun kolin Najeriya ta tabbatar da matakin da INEC ta ɗauka, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Twitter
Atiku ya gana da shugabannin ADC na jihohi
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gana da shugabannin jam’iyyar ADC na jihohi 36 da kuma na Abuja, a gidansa.

Kara karanta wannan
"Ƙila don ya ƙi APC ne": El Rufa'i ya yi tir da kai sunan Kwankwaso majalisar Amurka
Rahotanni sun nuna nuna an yi wannan zama ne a gidan Atiku da ke babbak birnin tarayya Abuja, inda duka tattauna batutuwa da fama kan shitun zaben 2027.
Shugabannin ADC sun ziyarci dan takarar shugaban kasar na PDP a zabe 2023 ne bisa jagorancin shugaban jam'iyyar na Kogi, Ogga Kingsley.
Asali: Legit.ng

