Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Fada da Ya Koma APC
- Gwamnan Kano, Alhaji Abba Yusuf ya sake jaddada dalilan da suka janyo ra'ayinsa har ya hakura da jam'iyyar NNPP da ta kawo shi mulki
- A bikin karbarsa zuwa APC da ya gudana a Kano a ranar Litinin 16 ga watan Fabrairu, 2026, gwamnan ya ce yanzu jiharsa ta shiga sahun gaba
- Ya ce Kano ta samu kujera a teburin yanke hukunci na ƙasa a maimakon a mayar da ita saniyar ware wajen manyan al'amura a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya bayyana a cewa yanzu za a fara dama wa da jihar yadda ya kamata bayan komawarsu zuwa jam'iyya mai mulki.
Ya bayyana haka ne a yayin taron tarbarsa da Shugaban APC na kasa Nentawe Yilwatda, Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Barau Jibrin suka halarta.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa gwamna ya ce sauya sheka zuwa APC ya sa Kano za ta samu babbar kujera a al'amuran kasa.
Abba ya ji dadin koma wa jam'iyyar APC
Arise News ta wallafa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda aka zaɓa a 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya yi murabus daga jam’iyyar a ranar 23 ga Janairu.
Ya danganta ficewarsa da rikice-rikicen cikin gida da kuma yawaitar shari’o’i da suka dabaibaye jam’iyyar, wanda ake ganin suna hana ruwa gudu.
Bayan murabus ɗin, ya shiga APC a hukumance ranar 25 ga Janairu 2026, a wani gagarumin biki da aka shirya a Fadar Gwamnati.
An karɓi gwamnan zuwa APC ne a hukumance ta hannun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Abin da Gwamna Abba ya ce
Da yake jawabi ga dubunnan magoya baya, gwamnan ya ce matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga muradin al’ummar Kano da kuma buƙatar samun kwanciyar hankali a harkokin mulki.
Ya ce ƙarƙashin manufar Shugaban Ƙasa, Najeriya na fuskantar sauye-sauye da ke buƙatar jihohi masu kishin ci gaba su kasance cikin tafiyar gwamnatin tarayya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce duk da sauyin jam’iyya, jajircewarsa wajen yin adalci da gudanar da mulki nagari ba zai sauya ba.
Ya bayyana cewa al’ummar Kano sun gaji da rigingimun siyasa marasa iyaka, suna son ganin ci gaba a fannin ababen more rayuwa, ilimi da tsaro.
A cewarsa, Kano jiha ce mai girma da muhimmanci kuma ci gabansa na ta’allaka ne da daidaituwa da haɗin kai domin samun damar cin moriyar tsare-tsaren ƙasa.
Kashim Shettima ya taya Abba murna
A baya, kun ji cewa Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana Kano a matsayin jiha mai tasirin siyasa da al’adu, wacce ta ke da muhimmin tasiri a Najeriya.
Ya ce duk lokacin da Kano ta yi magana, Najeriya na tsaya wa cak, ba don yawan jama’arta kaɗai ba, har ma da rawar da ta taka a tarihin siyasa, kasuwanci da al’adu.
Shettima taya Gwamna Abba Kabir Yusuf da magoya bayansa murna bisa abin da ya kira jarumtaka da hangen nesa na shiga APC, yana mai ba su tabbacin cikakken goyon bayan jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

