Shettima Ya Fadi Sakon Tinubu da Manyan Jiga Jigai Suka Tarbi Gwamna Abba zuwa APC a Kano

Shettima Ya Fadi Sakon Tinubu da Manyan Jiga Jigai Suka Tarbi Gwamna Abba zuwa APC a Kano

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya wakilci Bola Tinubu a taron tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC a Kano
  • Shettima ya isar da sakon Shugaba Tinubu na jajen ibtila'in da ya faru a kasuwar Singa ga Gwamna Abba da sauran wadanda abin ya shafa
  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Yelwatda Nentawe, Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Ganduje na cikin wadanda suka tarbi Abba Gida-Gida

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Manyan shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar APC, sun karɓi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa cikin jam’iyya a hukumance yau Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gagarumin taron karbar Abba da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tinubu ya kama hanyar zuwa Adamawa, Shettima ya tafi jihar Kano

Taron APC a Kano.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima manyan kusoshi a taron tarbar Gwamna Abba Kabir zuwa APC Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Manyan jiga-jigan APC sun tarbi Abba

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa taron ya tara dubban magoya baya da ’yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban sauyi a siyasar Kano.

Daga cikin waɗanda suka halarta akwai mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, shugaban APC na lasa, Nentawe Yilwatda da sohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma gwamnonin jihohin Jigawa, Kebbi, Kaduna, Sokoto da Imo, tare da sauran manyan shugabannin jam’iyya da ’yan majalisar tarayya, sun halarci taron.

Shettima ya isar da sakon Tinubu

Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana Kano a matsayin jiha mai muhimmanci a fagen siyasa da harkokin tattalin arziki

“Kano alama ce ta haɗin kan Najeriya. Duk lokacin da Kano ta yi magana, ƙasa baki ɗaya na sauraro, ba wai saboda yawan jama’arta kaɗai ba, har da rawar da ta taka a tarihin siyasa, kasuwanci da al’adu,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau

Ya taya Gwamna Abba da magoya bayansa murnar shiga APC, yana mai cewa mataki ne na hangen nesa da jarumtaka, tare da ba su tabbacin goyon bayan jam’iyya.

Taron APC.
Dubban mutane a gangamin maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC a Kano Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Tinubu ya jajantawa yan kasuwar Singa

Shettima ya kuma isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Tinubu kan gobarar da ta faru a Kasuwar Singa, inda ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da tallafin Naira biliyan 5 ga waɗanda lamarin ya shafa.

Ya ƙara da cewa Ƙungiyar Gwamnonin APC ma ta yi alƙawarin bayar da ƙarin tallafin kuɗi ga ’yan kasuwar da abin ya shafa.

“Kano jiha ce mai matuƙar muhimmanci da ba za ta kasance a gefe ba. Haɗuwarmu a yau ta ƙara mana ƙarfi wajen gina Najeriya mai haɗin kai da wadata,” in ji Shettima.

Gwamna Abba ya yaba da hadin kan Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan Abba Akbir Yusuf ya bayyana cewa an fara samun zaman lafiya da hadin kai a tsakanin shugabannin siyasa na jihar Kano.

Ya ve hakan na da alaka da addu'o'in da ake ci gaba da yi domin neman hadin kai, zaman lafiya, da ci gaba a Jihar Kano, wanda tuni suka fara samar da sakamako mai kyau.

Abba ua jaddada cewa nan ba da dadewa ba za a sasanta takaddamar Masarautar Kano cikin ruwan sanyi ta hanyar da za ta gamsar da dukkan bangarorin da abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262