Yadda Jama'a Suka Fito Zanga Zanga da El Rufa'i Ya Ziyarci EFCC

Yadda Jama'a Suka Fito Zanga Zanga da El Rufa'i Ya Ziyarci EFCC

  • A safiyar ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026, tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i ya cika alkawarin da ya dauka
  • Ya kai kansa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar nan bayan hukumar EFCC ta gayyace shi ya amsa wasu tambayoyi
  • Wasu masu zanga-zanga sun taru a hedkwatar hukumar yayin da lauyan El-Rufa'i ke ganin EFCC ta wuce makadi da rawa a kan tsohon gwamnan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Wasu gungun masu zanga-zanga sun dura a harabar hedikwatar Hukumar EFCC da ke Jabi a birnin Abuja.

Sun yi cikar kwari a hukumar EFCC jim kadan kafin isowar Malam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gurfanar da El Rufa'i a gaban kotu kan zargin kutsen wayar Ribadu

An yi zanga-zanga a kan tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i
Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun kasu gida biyu, inda wasu suka fito domin nuna goyon baya gare El-Rufa'i.

An yi zanga-zanga kan El-Rufa'i a Abuja

Jaridar Punch ta wallafa cewa wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi kira ga hukumar EFCC da ta bincike El-Rufa'i kan zarge-zargen da ake masa.

Yanayin ya dauki hankali ne yayin da aka hangi jami’an tsaro suna tsayawa bakin kofar shiga ofishin hukumar, suna kula da yadda jama’a ke shigowa da fita.

An ce an samu 'yar takaddama kadan lokacin da aka hana wasu daga cikin mutanen da suka raka El-Rufai shiga cikin ofishin hukumar.

EFCC ta gayyaci El-Rufa'i tun yana kasar waje
Shugaban EFCC na Najeriya Ola Olukayode Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya isa ofishin ne domin amsa gayyatar da aka ce an aike masa da ita tun yana kasar waje.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya amsa gayyata, zai kai kansa ofishin EFCC a yau

Wannan mataki ya biyo bayan yunkurin kama shi da aka yi a filin jirgin saman Abuja a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairu, 2026.

Lauyan El-Rufa'i ya fusata

Ubong Esop Akpan, lauyan El-Rufai, ya bayyana cewa an kai takardar gayyatar EFCC zuwa gidansa ne a lokacin da yake kasar waje.

A cewarsa:

“Gayyatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta isa gidan Malam Nasir El-Rufa'i ne a lokacin da ya ke kasar waje, wanda hakan ya hana shi amsa gayyatar ko zuwa ofishin EFCC."

Ya kara da cewa tun daga watan Disamban 2025 suka tuntubi hukumar a madadin sa, suna tabbatar da cewa zai bayyana da zarar ya dawo Najeriya.

Akpan ya kuma bayyana cewa babu wata hujja ta shari’a da ta dace da yunkurin kama tsohon gwamnan, yana mai cewa hakan ya saba da tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Lauyan ya bukaci a dakatar da duk wani yunkurin tsare El-Rufai ba bisa ka’ida ba, a mayar masa da fasfonsa, tare da neman gafara kan abin da ya kira take hakki.

Kara karanta wannan

Shigo da guba: DSS za ta titsiye El Rufa'i kan zargin da ya yi wa Ribadu

Atiku ya aika sako ga El-Rufa'i

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya taya Nasir El-Rufai murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya kira shi da jarumi kuma mutum mai ilimi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce ayyukan Malam Nasir El-Rufai suna nan a bayyane duk da tsangamar siyasa da yake fuskanta a yanzu haka.

A halin yanzu, El-Rufai ya na hannun hukumar EFCC, tun bayan da ya mika kansa ofishinsu na Abuja a safiyar yau Litinin bayan ya amsa gayyatar hukumar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng