An Kada Hantar Kwankwaso, Barau Ya Yi Alkawari ga Abba, Tinubu kan Zaben 2027
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi alkawarin samar wa yan takarar APC kuri'u masu yawa
- Ya ce shugabannin APC a Kano ta Arewa sun hada kai, sun kuma shirya tsaf domin tabbatar da nasara a dukkanin matakai
- Barau ya raba motoci 26 da babura 141 ga shugabannin jam’iyya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kara karfi da jawo kuri’u
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi magana game da zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Barau ya bayyana aniyarsa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf sun samu kuri’u masu yawa a 2027.

Source: Twitter
Kano: Matsayar da shugabannin APC suka cimma
Sanatan ya yi wannan jawabi ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyya a Kano, inda aka tattauna dabarun tunkarar babban zaben kamar yadda ya wallafa a X.
Barau ya ce shugabannin APC a Kano ta Arewa sun cimma matsaya daya tare da kudirin hada kai domin ganin jam’iyyar ta samu nasara.
Ya bayyana cewa taron an shirya shi ne domin kara dankon zumunci da hada kan mambobi kafin fara shirye-shiryen yakin neman zabe.
“Mun haɗe kuma mun mayar da hankali. Kano ta Arewa za ta yi tsayin daka wajen samar wa Shugaba Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ƙuri’u masu yawa.”
“Da yardar Allah, za mu kawo ƙuri’u masu yawa ga dukkanin ’yan takarar jam’iyyarmu a 2027.”

Source: Facebook
Barau ya yi abin alheri ga yan jam'iyya
A yayin taron, Sanata Barau Jibrin ya sanar da rabon motoci 26 da babura 141 ga shugabannin jam’iyya a kananan hukumomi 13 domin saukaka ayyuka.
Ya ce shugabanni za su samu motoci, yayin da sakatarori da sauran jiga-jigan jam’iyya za su karbi babura don taimakawa shirye-shirye.
“Tallafi ga shugabannin jam'iyya yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa tushe, har ila yau, haɗin kai da shirye-shirye, Kano ta Arewa za ta samu gagarumar nasara a 2027.”
- In ji Barau Jibrin

Kara karanta wannan
Tsohon yaron Ganduje ya fadi illar da tikitin Jonathan, Kwankwaso zai yi wa Tinubu
Wasu daga cikin mahalarta taron sun yaba da jagorancin Barau tare da alkawarin ba shi da sauran ’yan takara cikakken goyon baya.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki a Jihar Kano, Rt. Hon. Muhammad Bello Butu-Butu, ya ce yankin bai taba samun wakilci mai tasiri kamar na Barau Jibrin ba.
Ya bayyana cewa shugabannin kananan hukumomi da sauran mambobi sun kuduri aniyar aiki tukuru domin ganin Tinubu, Barau da Abba sun sake samun nasara.
'Abin da Tinubu ya fada wa jagororin APC'
Mun ba ku labarin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi magana kan shigowar Gwamna Abba Kabir zuwa jam'iyyar APC.
Sanata Barau ha bayyana cewa jagororin APC a Kano sun samu sako daga wajen Shugaba Bola Tinubu gabanin shigowar Abba cikin jam'iyyar.
Ya bayyana cewa tun da gwamnan na Kano ya riga ya shigo APC, za su ba shi dukkanin hadin kan da yake bukata.
Asali: Legit.ng
