Tuna Baya: Yadda INEC Ta Sauya Ranar Zaɓe a 2023 bayan Korafin Kiristoci a Najeriya
- An tuna yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sauya lokacin zabe bayan Kiristoci sun yi korafi kan shirin
- A shekarar 2003, INEC ta sauya ranar zaben gwamna da majalisar jiha bayan korafin Fastoci na Katolika kan karo da bikin Easter
- Kungiyar CBCN ta ce sanya zabe a ranar Asabar Mai Tsarki ya nuna rashin la’akari da mabiya Kirista masu cika ibada
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An samu ce-ce-ku-ce bayan hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta fitar da jadawalin zaben 2027.
Musulmai da dama sun yi korafi duba da yadda aka sanya ranar zaben a cikin watan Ramadan na shekarar 2027.

Source: Facebook
Yadda Kiristoci suka yi wa INEC bore
Sai dai a shekarar 2003 na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sauya ranar gudanar da zabe bayan korafin Fastoci na Katolika kan karo da Easter.
Tun farko, INEC ta sanya ranar 19 ga Afrilu, 2003 domin gudanar da zaben gwamna da na majalisar dokokin jiha a fadin Najeriya.
Sai dai ranar ta yi daidai da 'Holy Saturday' wato ranar Asabar Mai Tsarki kafin 'Easter Sunday', muhimmin lokaci a kalandar Kiristoci.
Kungiyar Fastocin na Katolika ta Najeriya (CBCN) ta bayyana cewa ranar da aka zaba ba ta dace ba, tana mai bukatar a sake nazari.
Fastocin sun yi gargadin cewa gudanar da zabe a ranar zai hana Kiristoci da dama cika hakkokinsu na addini da na kasa.
Sun roki Hukumar INEC da ta sauya ranar zaben domin tabbatar da hadin kai da mutunta bambancin addini a kasar.

Source: Twitter
Bayan shan matsai, INEC ta sauya ranar zabe
Korafe-korafen sun haifar da muhawara a tsakanin jama’a kan yadda za a daidaita jadawalin zabe da bukukuwan addini.
Bayan tuntubar bangarori daban-daban da matsin lamba daga jama’a, INEC ta sanar da sauya ranar zaben.
Daga bisani, hukumar ta mayar da zaben gwamna da na majalisar jiha zuwa wata sabuwar rana a cikin watan Afrilu din.
Maganganu sun biyo bayan saka ranar zabe
A halin yanzu, irin wannan muhawara ta sake kunno kai bayan sanar da jadawalin babban zaben shekarar 2027.
Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya sanar da ranakun zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya a wani taro a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ranakun na iya fadawa cikin watan azumin Ramadan, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Mohammed Haruna, kwamishinan kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai na INEC, ya ce jadawalin ya bi dokoki yadda ya kamata.
Sai dai ya kara da cewa hukumar na ci gaba da tuntuba, kuma za ta iya neman gyaran doka idan hakan ya zama dole.
Ya tabbatar da cewa duk wani sauyi da za a yi zai kasance cikin ka’idojin kundin tsarin mulki da dokokin kasa.
Ramadan: Majalisa za ta zauna kan zaben 2027
An ji cewa Majalisar wakilan tarayya ta shirya zaman gaggawa a mako mai zuwa kan ce-ce-ku-cen da ya barke bayan fitar da jadawalin zaben 2027.
A ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairu, 2026, INEC ta sanya ranakun zaben shugaban kasa, gwamnoni da yan Majalisar tarayya da na jihohi.
Sai dai ranakun da INEC ta sanya sun fada ne a cikin watan azumin Ramadan, lamarin da ya jawo suka daga Musulmai masu ibada a lokacin.
Asali: Legit.ng


