Ana Ruguza Allunan Tallata Tinubu a Zamfara, Ran Jam'iyyar APC Ya Baci
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi gargadi game da zargin ruguza allunan tallan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a sassan Zamfara
- Kakakin APC a jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau ne ya fitar da sanarwa yana gargadin cewa ba za su taba lamuntar lalata musu kayayyaki ba
- A bayanin da ya fitar, Yusuf Idris Gusau ya sanar da cewa a baya sun mika korafi ga jami'an tsaro amma duk da haka ba a daina musu barna ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Reshen jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ya nuna damuwa kan zargin ci gaba da cirewa da lalata allunan talla masu ɗauke da hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wata sanarwa da kakakin APC a Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, jam’iyyar ta ce ana zargin cewa irin waɗannan ayyuka sun daɗe suna faruwa.

Source: Facebook
Radio Nigeria Kaduna ya wallafa cewa sanarwar ta ce jam’iyyar ta riga ta kai ƙorafi ga hukumomin tsaro domin dakatar da abin da ta kira ayyuka masu alaƙa da siyasa da gwamnatin jihar ƙarƙashin PDP ke yi.
Korafin APC kan taba allunan Bola Tinubu
APC ta zargi cewa gwamnatin jihar Zamfara da cewa ta sake komawa lalata mata alluna, tana mai cewa ana amfani da hukumomin gwamnati.
Ta ce ana amfani da hukumar tsare-tsaren birane ta ZUREP domin aiwatar da ayyuka masu tayar da hankali da ka iya haddasa rikicin siyasa gabanin zaɓukan cikin gida na jam’iyyar da kuma babban zaɓen 2027.
Sanarwar ta ƙara da cewa, a ranar Laraba, jami’an hukumar sun yi yunƙurin cire wani allon talla mai ɗauke da hoton shugaban kasa tare da ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, da Sanata Abdulaziz Yari Abubakar.

Source: Facebook
Daily Post ta rahoto APC ta ce allon tallan, wanda yake a gaban gidan ministan da ke Gusau, ya tsira ne sakamakon daukin da jami’an tsaro da ke gadin gidan suka kai.
Kiran APC ga hukumomin gwamnatin Zamfara
Jam’iyyar ta sake kira ga hukumomin tsaro a jihar da su sa baki domin hana ci gaba da lalata kayayyakinta, wanda ta ce hakan raini ne ga ofishin shugaban kasa da kuma dimokuraɗiyyar.
APC ta yi gargaɗi cewa rashin bai wa shugaba Bola Ahmed Tinubu cikakken girmamawa da karramawa a matsayinsa na jagoran ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin sojoji ba zai samu amincewar jam’iyyar ba.
El-Rufa'i ya caccaki gwamnatin APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya caccaki gwamnatin APC da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta.
Ya bayyana cewa ya shirya damarar yaki da APC har sai sun kawar da ita a zaben shugaban kasar da za a yi a Najeriya a shekarar 2027.
Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi kwana daya bayan dawowa Najeriya daga kasar Masar da ya shafe kwanaki a can.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

