"Sai Mun Tashi Tsaye," Abin da El Rufai Ya Fadawa Atiku game da Tinubu a Abuja
- Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da jami'an tsaro suka yi yunkurin kama shi ya karbi bakuncin Atiku Abubakar a gidansa
- El-Rufai ya shaidawa Atiku cewa abin da ya faru da shi a filin jirgi ya kara tabbatar da cewa dole 'yan adawa su kafa gwamnati a 2027
- Tsohon gwamnan ya kuma fada wa Atiku cewa bai kamata su runtsa ba har sai sun kawar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa dole ne 'yan adawa su tashi tsaye domin kafa sabuwar gwamnati a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
A daren Alhamis, 12 ga Fabrairu, 2026, El-Rufai ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Alhaji Atiku Abubakar, bayan yunƙurin da jami'an tsaro suka yi na kama shi a Abuja.

Source: Twitter
Abin da El-Rufai ya fadawa Atiku
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa wannan dambarwa ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen tabbatar da cewa an kawar da Shugaba Bola Tinubu daga kan mulki, in ji rahoton Vanguard.
El-Rufai ya shaidawa Atiku cewa:
"Ranka ya daɗe, ina tabbatar maka cewa abin da ya faru yau ya ƙara fito da maganata ta cewa dole ne mu tashi tsaye, mu yi aiki tuƙuru.
"Ba za mu runtsa ba daga yanzu zuwa Maris din shekarar 2027, har sai mun cire wannan azzalumin daga ofis.
"Abin da ya faru a filin jirgi yau abin takaici ne, ba shi da amfani, sannan kuma wataƙila babban laifi ne ga dokokin ƙasarmu.
"Hukumomi suna da ƙa’idojin aiki, abin da na nema kawai shi ne su ba ni takardar gayyata sai in ziyarci ofishinsu da kaina.
"Amfani da hukumomin tsaro a matsayin reshen jam’iyyar siyasa babban kuskure ne ga gwamnatin da ta san cewa ba za a sake zaɓarta ba."
Bayani kan yunƙurin kama El-Rufai
El-Rufai ya zargi hukumar ICPC da yin amfani da jami'an DSS wajen yunƙurin 'sace' shi ba tare da wata takardar gayyata ta hukuma ba.
Ya bayyana cewa yayin da hukumar EFCC ta riga ta gayyace shi, hukumar ICPC ba ta tuntuɓe shi ba har sai a filin jirgi, in ji rahoton Tribune.
Lauyansa ya riga ya sanar da hukumar EFCC cewa zai bayyana a ofishinsu ranar Litinin da misalin ƙarfe 10:00 na safe domin amsa tambayoyi.
El-Rufai ya jefa zargi kan Nuhu Ribadu
Tsohon gwamnan ya zargi shugaban hukumar ICPC da yin aiki bisa umarnin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, domin kuntata masa.
Ya yi gargaɗin cewa yin amfani da jami'an tsaro don cimma manufar siyasa yana ruguza martabar hukumomin dimokuradiyya da kuma dokokin ƙasar Najeriya.
A cewarsa, gwamnatin Shugaba Tinubu tana ƙoƙarin ci gaba da rike madafun iko ta kowane hali saboda ta san cewa ba za ta kai labari a zaɓe ba.
Kalli bidiyon ziyarar Atiku gidan El-Rufai, wacce tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X:
Fasinjoji sun hana a kama El-Rufai
Tun da fari, mun ruwaito cewa, jami'an tsaro sub yi yunkurin kama tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai a filin jirgin saman Abuja.
Sai dai, jami'an tsaron sun gamu da cikas domin kuwa fasinjoji da magoya bayan tsohon gwamnan sun tsaya kai da fata don ganin ba a tafi da shi ba.
A filin jirgin, Malam Nasir El-Rufai ya kalubalanci jami'an tsaron da su mika masa takardar gayyata maimakon su yi kokarin kama shi ta karfin tsiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


