Da Sake: ADC Ta Dura a kan Gwamnati a kan Yunkurin Kama El Rufa'i
- Jam'iyyar adawa ta ADC ta yi tir da yunkurin kama jigo a cikinta kuma tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i a filin jirgi
- Jam’iyyar ta zargi gwamnatin APC da amfani da hukuma wajen tsoratar da ‘yan adawa domin ta dakile karfinsu a Najeriya
- Ta bukaci hukumomin tsaro su mutunta doka da kundin tsarin mulki wajen aikinsu na yaki da cin hanci da rashawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar hamayya ta ADC ta yi kakkausar suka kan yunkurin da wasu jami’an tsaro suka yi na kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
A ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu ne jami'an tsaro suka dura a filin jirgin saman Abuja inda suka yi yunkurin awon gaba da El-Rufa'i, amma daga bisani jama'a suka yi dafifi aka hana su.

Source: Facebook
A wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ADC na Allah wadai da wannan abu.
ADC ta yi tir da gwamnatin Najeriya
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa ADC na ganin wannan abu da ya faru ba kuskure ba ne, illa wata alama ce ta yadda ake kokarin matsa wa da dakile yan adawa tare da matsa masu lamba.
Sanarwar ta ce:
ADC ta yi tir da yunkurin jami'an tsaro na kama tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i a filin girni, wanda ya jawo damuwa da tambayoyi a kan wannan gagarumin take kundin tsarin mulki da dimokuradiyya."

Source: Twitter
ADC ta yi zargin cewa akwai alamun nuna wariya wajen aiwatar da doka, inda ake tsananta bincike kan shugabannin adawa.
Ta kara da cewa ana barin wasu da ake zargi da cin hanci, kuma suna ci gaba da sharafinsu wajen shiga jam'iyya mai mulki a dama da su.
Jam’iyyar ta ce idan har ba a gabatar da wata takardar kama ko sammaci ba a lokacin da aka yi yunkurin kama El-Rufa’i, to hakan na nuna cewa ba a bi ka’idojin doka ba.
Kiran ADC ga hukumomi
ADC ta jaddada kudirinta na kare gaskiya, rikon amana da bin doka, tana mai cewa ba za ta amince da muzgunawa ko tsoratar da shugabanni saboda ra’ayinsu na siyasa ba.
Ta bukaci hukumomin tsaro da takwarorinsu da su kasance masu bin ƙa’ida da kundin tsarin mulki a dukkannin matakan da suke dauka.
Jam’iyyar ta kuma gargadi gwamnatin APC karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu da ta fahimci muzgunawa yan adawa ba ya nufin karfi a dimokuradiyya.
ADC ta ce za ta ci gaba da sanya ido kan duk wani lamari da zai iya barazana ga tsarin dimokuradiyya.
Atiku ya magantu kan yunkurin kama El-Rufa'i
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi magana kan yunkurin cafke Malam Nasiru El-Rufa'i da aka yi a birnin tarayya Abuja.
Atiku Abubakar, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne ya yi zargin cewa hukumar EFCC da ke da alhakin yaki da cin hanci da rashawa ta fi mayar da hankali kan 'yan adawa.
Ya yi gargadi da cewa hukumar yaki da cin hanci da rashata ta kasa za ta rasa kima a wajen jama'ar Najeriya idan ta ci gaba da farautar mutanen da ke adawa da gwamnatin Bola Tinubu
Asali: Legit.ng

