'Abin da Ya Sa Dole Arewa Ta Zabi Tinubu a 2027'; Shugaban APC

'Abin da Ya Sa Dole Arewa Ta Zabi Tinubu a 2027'; Shugaban APC

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya halarci wani gagarumin taron siyasa da aka shirya a jihar Nasarawa
  • Farfesa Nentawe ya yi jawabi a wurin taron inda ya lissafo manyan ayyukan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ke yi a Arewacin Najeriya
  • Shugaban na APC ya kuma bayyana dalilin da ya sanya dole yankin Arewa ya goyawa shugaban kasar baya a zabe mai zuwa na 2027

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Nasarawa - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kwararo yabo ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Farfesa Nentawe ya jinjina wa Shugaba Tinubu kan abin da ya kira ƙoƙarin kai Najeriya zuwa matsayi mai girma tun bayan karbar mulki a shekarar 2023.

Farfesa Nentawe ya halarci taron APC a Nasarawa
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taron APC a Nasarawa Hoto: Gov Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Farfesa Nentawe ya yi wannan bayani ne a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

An kada hantar Kwankwaso, Barau ya yi alkawari ga Abba, Tinubu kan zaben 2027

Ya yi bayanin ne yayin wani taron nuna goyon baya da aka shirya domin nuna godiya ga shugaban kasa da Gwamna Abdullahi Sule kan abin da masu shirya taron suka kira ayyukansu na gari.

Shugaban APC ya fadi ayyukan Tinubu a Arewa

Farfesa Nentawe ya kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta fi fifita yankin Arewa fiye da kowane yanki na kasar nan ta fuskar ayyukan ci gaba da ƙarfafa gwiwar al’umma.

Shugaban na APC ya buƙaci ’yan Arewa da su saka wa shugaban ta hanyar goyon bayan takararsa na sake tsayawa zaɓe a shekarar 2027.

"Shugaban kasa ya nuna cewa Najeriya za ta iya zama tsintsiya ɗaya madaurinta ɗaya. Ya nuna cewa gwamnati za ta iya zama mai haɗa kan kowa, kuma ya nuna cewa gwamnati za ta iya zama mai tsayin daka. Shi ya sa muke a wannan wajen."
“Muna da hanyar da ta tashi daga Sokoto zuwa Badagry, wadda za ta samar da madatsun ruwa sama da 60 don ban-ruwa. Za ta samar da ci gaban noma, lantarki, da tsaftataccen ruwa. Wannan shi ne abin da shhugaban kasa yake samar mana a Arewa."

Kara karanta wannan

Jigon APC ya tono abin da aka rufe, ya fadi abin da Tinubu ke tsoro game da zaben 2027

“Shugaban kasa yana samar da layukan dogo na jirgin kasa, wanda zai tashi daga Abuja zuwa Kano har zuwa Jamhuriyar Nijar."
"Ga dukkanmu a Arewa, hakan na nufin za mu zama masu shigo da kaya da fitar da su, domin daukacin yankin Arewacin Sudan, Burkina Faso, da Chadi za su dogara ne da mu wajen shigo da kayayyakinsu."
“Dukkan waɗannan ayyuka shugaban kasa ne yake yin su. Shi ya sa zai zama rashin adalci ga Arewa idan ba mu ba shi goyon baya ba, domin ba kowa ne zai iya samun ƙarfin gudanar da waɗannan ayyuka a gare mu ba kuma."
"Goyon bayan shugaban kasa ya zama dole ga Arewa saboda abubuwan da ya samar, abin da yake yi, da kuma abin da zai yi wa daukacin yankin.”

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Shugaban APC ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Farfesa Nentawe Yilwatda a wajen taron jam'iyyar APC a Nasarawa Hoto: @APCNewMedia
Source: Twitter

Nentawe ya jinjina wa Gwamnan Nasarawa

Yayin da yake karbar dubun-dubatar mutanen da suka sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa zuwa APC, shugaban ya kuma jinjina wa Gwamna Sule kan yadda yake samar da shugabanci na gari a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan samun mukami, tsohon mai sukar Tinubu ya fadi abin da zai sa ya zarce a 2027

Ya nuna godiyarsa ga ayyukan samar da ababen more rayuwa a daukacin ƙananan hukumomin jihar guda 13, waɗanda suka haɗa da gadojin sama, hanyoyin cikin gari da na karkara, makarantu, asibitoci, da filin jirgin kasa da sauransu.

Shafin @APCNewMedia ya sanya bidiyon jawabin da shugaban na APC ya yi a wajen taron.

Kujerarsa yake karewa

Wani mazaunin jihar Katsina, Kabir Usman, ya bayyana cewa shugaban na APC magana kawai yake irin ta siyasa kan sake zaben shugaban kasar.

"Surutu ne kawai irin na siyasa cewa dole ne Arewa ta sake zaben Shugaba Tinubu a 2027. Wane ci gaba ya kawowa yankin? An bar talakawa kawai cikin wahala da kunci."
"Me ye amfanin titi yayin da ake kashe mutane da raba su da matsugansu. Ai wannan gwamnatin ta kasa samar da muhimmin abu ga talaka, wato tsaro."
"Lokaci zai zama alkali amma mu ba mu ga wani abu da gwamnatin nan ta yi ba wanda zai sanya mu sake zabenta."

- Kabir Usman

Tinubu zai tarbi Gwamna Abba zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tarbi Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Sheikh Pakistan ya fadi dalilin murabus daga shugabancin NAHCON

Mai girma Bola Tinubu zai tarbi gwamnan ne a wani gagarumin biki da aka shirya gudanarwa a babban birnin jihar Kano.

Shugaban jam'iyyar APC na Kano ya bayyama cewa an kaddamar da kwamitocin da za su kula da shirin tarbar gwamnan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng