Dan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC, Ya Hadu da Gwamnan Gombe

Dan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC, Ya Hadu da Gwamnan Gombe

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Gombe ta gamu da cikas bayan wani dan majalisar wakilan tarayya ya fice daga cikinta
  • 'Dan majalisar wakilan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai rinjaye a majalisar tare da yin rajista don zama cikakken mamba
  • Bayan shigarsa APC, dan majalisar ya gana da Gwamna Inuwa Yahaya wanda ya ba shi tabbacin cewa za a yi masa adalci a jam'iyyar

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani mamba a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Abdullahi El-Rasheed (Bala Kelly), ya fice daga daga jam’iyyar PDP a jihar Gombe.

'Dan majalisar ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC bayan ya fice daga PDP mai adawa a jihar Gombe.

Dan majalisar wakilai na PDP a Gombe ya koma APC
Hon Abdullahi El-Rasheed tare da Gwamna Inuwa Yahaya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, Ismaila Uba Misilli ya fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2026 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar wakilai daga Kano na tsaka mai wuya, NNPP na neman raba shi da mukaminsa

'Dan majalisa ya ziyarci Gwamna Inuwa

Dan majalisar, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Dukku/Nafada, ya sanar da komawarsa APC ne yayin da ya ziyarci Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a Abuja.

Ismaila Uba Misilli ya ce yayin ziyarar, Hon. El-Rasheed ya mika wa gwamnan katin zama dan jam’iyyar APC, wanda ya karba daga mazabarsa da ke karamar hukumar Dukku yayin aikin rijistar ’ya’yan jam’iyya ta yanar gizo da ake gudanarwa a yanzu.

Hon. Bala Kelly ya yaba wa jam'iyyar APC

'Dan majalisar ya danganta matakinsa na shiga APC da salon jagoranci na gari na Gwamna Inuwa Yahaya, da manufofinsa masu alaka da jin dadin jama'a da kuma ayyukan ci gaba da ake gani a fadin jihar Gombe, da kuma shirin gyara na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bala Kelly ya siffanta APC a matsayin wani dandali da ke da kyakkyawan matsayi na samar da ci gaba mai dorewa da shugabanci na gari, inda ya yi alkawarin cikakkiyar biyayya da kishin jam’iyyar da shugabancinta a karkashin Gwamna Inuwa Yahaya.

Kara karanta wannan

'Dan majalisar Sokoto ya lale Naira miliyan 100, ya ba yara 2000 tallafin karatu

Me Gwamna Inuwa ya gaya masa?

A nasa martanin, Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da Hon. El-Rasheed zuwa cikin "masu ra'ayin ci gaba," inda ya yaba da jarumtarsa da kuma kwarin gwiwarsa.[

Gwamna Inuwa ya tarbi dan majalisar da ya koma APC
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya tare da Hon. Abdullahi El-Rasheed Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Gwamnan ya tabbatar masa da cewa za a ba shi dukkan damammaki daidai da kowa, sannan ya bukace shi da ya yi aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar domin ciyar da ajandar ci gaba ta APC, don amfanin mutanen mazabarsa, jihar Gombe, da ma Najeriya baki daya.

Sanatoci sun fice daga PDP zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu sanatoci na jam'iyyar PDP a jihar Taraba sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a shekarar nan.

Sanata Haruna Manu (Taraba ta Tsakiya) da Sanata Shuaibu Isa Lau (Taraba ta Arewa) bayyana cewa matsalolin cikin gida na PDP ya sanya suka fice daga jam'iyyar.

Sun jaddada cewa za su fi samun damar gudanar da ayyukan ci gaba ga al'ummarsa idan yana ƙarƙashin inuwar jam'iyya mai mulki ta APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng