‘Son Zuciya ne’: Dan APC Ya Soki Majalisar Shari’a kan Neman Cire Shugaban INEC
- Wani dan jam'iyyar APC ya bukaci Dr. Bashir Aliyu ya fito takara maimakon neman a sauke Shugaban hukumar zaben ta INEC
- Dr. Sani Ahmad Zangina ya ce kiraye-kirayen cire shugaban INEC ba su dace ba, yana mai cewa kishin jama’a ne ya sa ya yi magana
- Zangina ya musanta alaka da shugaban hukumar INEC, ya bukaci a rika duba al’amura da adalci da gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Fitaccen dan jam’iyyar APC, Dr. Sani Ahmad Zangina, ya mayar da martani mai zafi game da kiran sai an cire sabon shugaban INEC, Joash Amupitan.
Zangina ya yi kira ga Dr. Bashir Aliyu akan ya fito takara, ya gwada nasa kishin, wajen kawo sauyi maimakon kira akan a sauke shugaban.

Source: Facebook
Dan APC ya kare shugaban INEC
Dan gwagwarmaya kuma mai goyon bayan jam'iyyar APC ya bayyana haka a yayin hira da DCL Hausa wanda ta wallafa a Facebook.
Ya bayyana cewa kiraye-kirayen neman cire Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ba su dace ba, yana mai cewa hakan abin kunya ne ga wasu daga cikin jagororin Arewa.
Dr. Zangina ya ce abin da Shugaban INEC ya yi na rubuta bayani ko bayyana damuwa kan al’ummarsa bai zama laifi ba, domin a cewarsa kishin jama’arsa ne ya motsa shi.
Zangina ya fadawa wakilin Legit Hausa cewa Arewa, musamman al’ummar Musulmi, su ne suka fi fuskantar barazanar rashin tsaro, amma duk da haka koke-kokensu ba sa samun kulawar da ta dace.
“A kullum malamanmu da sarakunanmu sufi chanchanta su mika halin da Yankin su ciki, amma har yanzu babu wani kokari na isar da matsalolin yadda ya kamata.
Don haka idan wani ya dauki matakin isar da koken mutanensa, ba na ganin laifinsa ko kadan."
- Iin ji Zangina

Source: Twitter
Dr. Zangina ya musanta alaka da Amupitan

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka Trump ya hango abin da zai sanya ya shiga aljanna bayan ya fara cire rai
Sai dai Zangina ya nesanta kansa daga duk wani zargi da ke cewa yana da alaka ta kusa da Shugaban INEC.
Ya jaddada cewa bai taba saninsa ba, amma yana ganin idan ana magana kan adalci, dole ne a fadi gaskiya ko da kan waye ne.
Ya kuma bukaci a rika duba al’amura cikin adalci da gaskiya, ba tare da son rai ko nuna bangaranci ba, domin hakan ne kawai zai taimaka wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a kasa.
An fadi hatsarin zaman shugaban INEC
A wani labarin Majalisar ƙoli kan harkokin shari’ar musulunci a Najeriya ta sake nanata kiranta na a tsige shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan, tana mai cewa ba zai iya yin adalci ba.
Majalisar ta ce kiran ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci, sai dai yana da nasaba da halayya, nagarta da wasu kalamai da ta ce shugaban INEC ya taɓa furtawa a baya.
Ta jaddada cewa shugabancin hukumar zaɓe ta INEC na buƙatar mutumin da ba ya nuna wariya, bambanci ko kiyayya ga wani bangare na al’ummar da ke zaune a Najeriya.
Asali: Legit.ng
