Abuja, Kano da Wasu Jihohi 3 da INEC za Ta Yi Zabe a 2026

Abuja, Kano da Wasu Jihohi 3 da INEC za Ta Yi Zabe a 2026

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa za ta jagoranci gudanar da zabe a wasu jihohi da yankunan Najeriya da suka hada da Kano a 2026.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na shirin gudanar da zabe a wasu jihohi da yankunan kasar nan a 2026.

INEC za ta jagoranci zaben gwamna a wasu jihohi da kuma zaben cike gibi bayan rasuwar 'yan majalisar jihar guda biyu a jihar Kano.

Jami'an INEC na bakin aiki a Anambra
Wasu jami'an INEC a zaben da aka yi a Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin jihohi da yankunan da hukumar INEC za ta shirya zabe tare da jagorantarsa a 2026.

1. Hukumar INEC za ta yi zabe a Abuja

Hukumar INEC ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓe a dukkan kananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ramadan na karatowa, za a yi gyaran iskar gas da zai rage wutar lantarki a Najeriya

INEC ta ce za a gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar, 21 ga Faburairu, 2026, da ƙarfe 8:30 na safe. Za a yi zaɓen a dukkan rumfunan zaɓe da ke faɗin Abuja.

Taron 'yan ADC a Abuja
Atiku Abubakar a kamfen din ADC a shirin zaben Abuja. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

2. Za a yi zabe a Rivers a 2026

Hukumar zaɓe ta sanar da za a gudanar da zaɓen cike gurbi a mazabun Ahoada Ta Gabas II da Khana II na Majalisar Dokokin Jihar Rivers.

Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar, 21 ga Faburairu, 2026, da ƙarfe 8:30 na safe a yankunan da aka ambata.

Yadda aka yi zaben Anambra
Masu kada kuri'a a zaben Anambra da aka yi a 2025. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

INEC ta bayyana cewa tana nan daram kan kudurinta na tabbatar da sahihin zaɓe mai cike gaskiya da adalci a wani sakon da ta wallafa a Facebook.

3. INEC za ta gudanar da zabe a Kano

Kamar jihar Rivers, hukumar zabe ta sanar da cewa za ta gudanar da zaben cike gibi bayan rasuwar 'yan majalisar Kano biyu a 2025.

Daily Trust ta rahoto cewa jam’iyyun ADC da PDP a Kano sun sanar da cewa ba za su shiga zaɓen da aka shirya yi a ranar 21 ga Faburairun 2026 ba.

Kara karanta wannan

Ana neman sauke Amupitan, INEC ta gabatar da kasafin kudin N873bn don zaben 2027

Jami'an INEC na tantance masu zabe
Masu zabe, jami'an NSCDC da na INEC a wajen zabe. Hoto: INEC Nigeria
Source: Depositphotos

Shugaban ADC na Jihar Kano, Musa Shu’aibu Ungoggo, ya ce jam’iyyarsu ta yanke shawarar kaurace wa zaɓen ne saboda ba ta da kwarin gwiwa kan sahihancin tsarin gudanar da shi.

Jam'iyyar NNPP da ke karkashin jagorancin Sanata Rabiu Kwankwaso ta sanar da ba 'ya'yan 'yan majalisar da suka rasu takara kafin Abba Kabir Yusuf ya koma APC mai mulki a Najeriya.

4. INEC za ta yi zaben gwamna a Ekiti

Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar cewa za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti ranar Asabar, 20 ga Yuli, 2026.

Katin zabe da hukumar INEC ta tanada
Katin zabe da INEC ke samarwa a Najeriya. Hoto: INEC Nigeria
Source: UGC

Bayanai sun nuna cewa shirye-shiryen gudanar da zaben sun fara nisa yayin da INEC ta saki sunayen 'yan takarar da za su fafata da juna.

5. Za a yi zaben Osun a 2026

Watanni bayan gudanar da zaben Osun, hukumar INEC za ta wuce jihar Osun domin gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026.

Kara karanta wannan

Rana ta baci: An kama 'yan fashi dauke da kayan satan miliyoyin Naira a Jigawa

Gwamna Ademola Adeleke a ofis
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke. Hoto: Osun State Government
Source: Twitter

Yayin da aka fara shirye-shiryen zaben, gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun da zai nemi tazarce ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar Accord.

An nemi a tsige shugaban INEC

A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin Shari'a na kasa ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban INEC.

Kwamitin ya bayyana cewa ya nemi sauke Farfesa Joash Amupitan ne saboda kiyayya da ya nunawa al'ummar Musulmi a Najeriya.

Sheikh Bashir Aliyu Umar ya bayyana cewa ba za a amince da samun adalci a zaben da wanda ya nuna adawa da Musulmai zai jagoranta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng