Amaechi Ya Ba ADC Hanyoyi 3 da Za Ta Fitar da Dan Takarar da Zai Kara da Tinubu a 2027

Amaechi Ya Ba ADC Hanyoyi 3 da Za Ta Fitar da Dan Takarar da Zai Kara da Tinubu a 2027

  • Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi tsokaci kan batun fitar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta ADC
  • Amaechi ya bayyana cewa zai yi wuya a tallata dan takarar shugaban kasa na ADC daga Arewa a Kudancin Najeriya
  • Tsohon Ministan ya ba jam'iyyar shawarar abubuwan da ta duba wajen fitar da dan takarar da zai gwaba da Mai girma Bola Tinubu a zaben 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ja kunnen jam'iyyar ADC dangane da fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Rotimi Amaechi ya yi gargadin cewa zai iya zama abu mai wahala ga jam’iyyar ADC ta tallata dan takarar shugaban kasa daga Arewa ga masu zabe a Kudancin Najeriya.

Amaechi ya ja kunnen ADC kan dan takarar shugaban kasa a 2027
Rotimi Chibuike Amaechi, tsohon Ministan sufuri a Najeriya Hoto: Rt Hon Chibuike R. Amaechi
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Amaechi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a Kano ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Sanata ya shawarci Musulmi kan yadda za su kalubalanci malamai

Me Amaechi ya ce kan dan takarar ADC?

Amaechi ya amsa tambayoyi kan ko zai marawa duk dan takarar da ya fito daga jam’iyyar ADC baya.

Ya ce a shirye yake ya marawa dan takarar jam’iyyar baya, amma ya jaddada cewa akwai bukatar daukar matakai na dabara da suka zama dole domin samun karbuwa a kasa da kuma nasarar zabe.

“Zan marawa duk wanda ya yi nasara baya. Amma kuma ina ba ADC shawara da su duba da kyau su gano mutumin da ya fi dacewa wanda zai iya gamsar da ’yan Najeriya cewa abubuwa za su sauya.”

- Rotimi Amaechi

Wace shawara Amaechi ya ba ADC?

Ya bayyana cewa dole ne jam’iyyar ta yi la’akari da muhimman abubuwa guda uku wajen zabar dan takarar shugaban kasa: kwarewa, shekaru, da kuma yadda raba madafun iko yake a kasar a halin yanzu.

“Na farko shi ne kwarewa. Na biyu shi ne shekaru. Na uku, wanda shi ne batu na karshe, shi ne girmama dokar da ba a rubuta ba ta raba mulki wadda a yanzu take a Kudu."

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Amaechi ya tafi da dansa wajen zanga zanga a majalisar dattawa, ya fadi dalili

- Rotimi Amaechi

A cewarsa, amincewa da tsarin karba-karba na mulki a yanzu zai saukaka wa ’yan siyasa da masu zabe a Kudu damar hada kai a bayan jam’iyyar, jaridar Leadership ta dauko labarin.

“Ya kamata su kammala wannan sannan su mika mulki ga Arewa. Hakan zai saukaka wa mu da muke daga Kudu mu ce za mu fafata saboda Arewa ta ce, ‘ku gama duk wannan,’”

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya ja kunnen ADC

Amaechi ya yi gargadin cewa tsayar da dan takara daga Arewa a daidai lokacin da mutane da dama a Kudu suka yi imanin cewa ya kamata mulki ya zauna a Kudu na iya raunana karbuwar ADC a yankin.

“Idan kuka zabi wani daga Arewa, ba na nufin ba za mu yi kamfe ba, amma zai yi wahala mu gamsar da Kudu su bar mulki saboda za su tambayi Arewa, ‘Me ya sa sai idan mulki ya zo Kudu ne ake samun matsala?’”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya ba jam'iyyar ADC shawara kan zaben 2027
Tsohon Ministan sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi Hoto: Rt Hon Chibuike R. Amaechi
Source: Twitter

Zai goyi bayan dan takarar ADC

Duk da wadannan korafe-korafe nasa, Amaechi ya sake jaddada kudurinsa na tabbatar da hadin kan jam’iyyar, inda ya ce zai marawa duk wanda ya yi nasara a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC baya, ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.

“Ko dan Kudu ne ko dan Arewa hakan ba shi ne a gaba ba, zan marawa duk wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani baya."

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya je zanga-zanga a majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya je wurin zanga-zanga kan dokar zabe a majalisar tarayya.

Rotimi Amaechi ya halarci zanga-zangar ne tare da babban dansa domin nuna adawa da matakin majalisar dattawa na kin amincewa da tura sakamakon zabe ta yanar gizo.

Amaechi ya bayyana cewa ya kamata shugabanni su kasance a sahun gaba a manyan zanga-zanga kuma su rika saka iyalansu a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng