Shugaban Tafiyar Kwankwasiyya Ya Rasu, Kwankwaso Ya Kadu da Rashin Jajirtacce

Shugaban Tafiyar Kwankwasiyya Ya Rasu, Kwankwaso Ya Kadu da Rashin Jajirtacce

  • An shiga jimami bayan sanar da rasuwar wani daga cikin shugabannin tafiyar Kwankwasiyya a jihar Katsina wanda ya ba da gudunmawa
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna takaici bayan samun labarin rasuwar marigayin inda ya yaba da jajircewarsa kan siyasa
  • Mutane sun yaba da jajircewarsa, sadaukarwarsa da rawar da ya taka wajen bunƙasa tafiyar Kwankwasiyya da walwalar al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - An bayyana matuƙar jimami bayan rasuwar Alhaji Muhammad Nasir Isah Tsauri, Shugaban Tafiyar Kwankwasiyya a Jihar Katsina.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na daga cikin wadanda suka nuna damuwa game da rashin dattijon da ya ba tafiyarsu gudunmawa sosai wanda ya ce ba za a manta ba.

Kwankwaso ya yi jimamin mutuwar shugaban Kwankwasiyya
Jagoran darikar Kwankwasiyya a Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso ya yi alhinin rasuwar Shugaban Kwankwasiyya

Jagoran Kwankwasiyya a Najeriya baki daya ya bayyana haka ne a jiya Litinin 9 ga watan Faburairun 2026 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fita kasar waje, ya yi magana kan sauya shekar Abba Kabir

Kwankwaso ya ce marigayin ya kasance mutum mai jajircewa da sadaukarwa, wanda ya ba da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa tafiyar Kwankwasiyya da kuma inganta walwalar al’ummar jihar Katsina.

'Ba za a manta da marigayin ba' - Kwankwaso

Madugu ya ce gudunmawar da ya bayar da hidimar da ya yi wa jama’a ba za a taɓa mantawa da su ba a tarihin siyasar darikar da suke bi.

Tsohon gwamnan ya ce marigayin ya bar tarihi mai kyau wanda zai ci gaba da zama abin koyi da ƙarfafa gwiwa ga mabiya tafiyar.

Daga bisani, jagoran Kwankwasiyya ya yi wa marigayin addu'o'i tare da ba iyalansa hakurin jure wannan rashi na jajirtacce da aka yi.

Kwankwaso ya yi addu'o'i ga shugaban Kwankwasiyya a Katsina
Sanata Rabiu Kwankwaso da Shugaban Tafiyar Kwankwasiyya a Katsina da ya rasu, Alhaji Muhammad Nasir Isah Tsauri. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Addu'o'in Rabiu Kwankwaso ga dattijon

'Dan siyasar ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan marigayin, ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi a Aljannar Firdaus, tare da bai wa iyalansa da al’ummar Katsina haƙurin jure wannan babban rashi.

Kwankwaso ya ce:

"Na shiga matuƙar jimami da rasuwar Alhaji Muhammad Nasir Isah Tsauri, Shugaban Tafiyar Kwankwasiyya a Jihar Katsina.
"Jajircewarsa, sadaukarwarsa ba tare da son kai ba, da kuma gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa tafiyarmu da walwalar al’ummarmu za su ci gaba da kasancewa a zukatanmu tare da ba mu ƙarfafa gwiwa a ko da yaushe.

Kara karanta wannan

Za a samu sauki, Tinubu ya amince a bude iyakar Najeriya da Nijar don kasuwanci

"Allah Maɗaukakin Sarki ya jiƙan marigayin, ya sa ya huta na har abada a Aljannar Firdaus mai alfarma."

Kwankwaso ya magantu kan harin Kwara

Mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da jimamin kisan gillar da 'yan ta'adda suka yi wa wasu mutane a kauyukan jihar Kwara wanda aka yi asara rayukan Musulmai da dama.

Hare-haren ta'addancin sun jawo asarar rayuka kusa da 200 na mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar da ke fama da hare-haren yan ta'adda.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bi sahun yin Allah wadai kan mummunan harin, tare da ba da shawararsa ga gwamnatin tarayya kan yadda za ta dakile yawan kai hari a kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.