El-Rufai Ya Yi Gajeren Tsokaci kan Rikicinsa da Uba Sani da Sabanin Kwankwaso da Abba

El-Rufai Ya Yi Gajeren Tsokaci kan Rikicinsa da Uba Sani da Sabanin Kwankwaso da Abba

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ba shi da alaƙar ubangida da yaronsa a siyasa da Gwamna Uba Sani
  • Ya jaddada adawarsa ga tsarin da ya ke kai na adawa da siyasar uban gida a Najeriya, tare da karin haske a kan alakarsa da Uba
  • Tsohon gwamnan ya ce bai taɓa kiran magajinsa ba tun bayan barin mulki, wanda ke kara jaddada matsayarsa a kan siyasar uban gida

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya karyata ikirarin cewa shi ne ubangidan siyasar magajinsa, Gwamna Uba Sani.

Ya jaddada cewa ba shi da sha’awar tsoma baki ko sarrafa duk wani wanda zai gaje shi bayan barin mulkin jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Zance ya fito: El Rufai ya haska abin da ya jawo sabani tsakaninsa da Tinubu

Nasir El-Rufa'i ya ce babu ruwansa da Uba Sani
Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i tare da Uba Sani Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a Trust TV a ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairu, 2026, wanda OurFavDoc online ya wallafa a shafin X.

El-Rufa'i ya fayyace alakarsa da Uba Sani

Jaridar Leadership ta wallafa cewa tsohon Gwamna El-Rufa'i ya yi magana kai tsaye kan rade-radin da ke yawo game da alaƙarsa da gwamnan Kaduna na yanzu.

Ya ce:

“Gwamna Uba Sani ba yarona ba ne a siyasa. Ban damu da magajina ba. Ba ni da sha’awar zama ubangida. Ban kira Uba Sani tun bayan barin ofis ba. Ba ni da wata alaƙa da shi.”

El-Rufa'i ya kuma amsa tambayoyi kan rikice-rikicen da ke yawan faruwa tsakanin ubangidan siyasa da yaransu.

Ya ce ana yawan kambama lamarin fiye da yadda ya kamata, kuma karfin iko na canjawa da zarar an sauya wanda ke mulki.

Ya ce wani tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taɓa faɗa masa cewa:

Kara karanta wannan

Akpabio: El Rufa'i ya zargi Shugaban Majalisa da zama alaƙaƙai wajen gyara dokar zabe

“Ko da ɗanka na jini ne ya zauna a kujerar iko, rana ta farko zai gaishe ka a matsayin uba, rana ta biyu zai zauna a kujerarsa, amma rana ta uku, idan ba ka gaishe shi da girmamawa ba, abubuwa marasa daɗi na iya faruwa.”

Tsokacin El-Rufa'i kan Abba da Kwankwaso

El-Rufai ya ce wannan darasi ne da ya koya tun da wuri, wanda ya sa ya tsani tsarin uban gida a siyasa tun fil’azal.

“Saboda haka, ban taɓa yarda da ubangida ba. Ko kaɗan. Na kasance mai fito-na-fito wajen adawa da shi,” in ji shi.

Tsohon gwamnan ya tuno yadda kalamansa kan siyasar ubangida suka jawo masa suka, musamman daga wasu ‘yan siyasa a Jihar Legas.

Ya ce:

“Na je Legas na amsa tambayoyi kan siyasar ubangida har aka rika kai min hari. ‘Yan gungun Tinubu suka taso ni a gaba saboda sun ɗauka ina nufinsa. Amma ina magana ne kan manufa."

Game da barinsa gidan gwamnatin Kaduna, El-Rufai ya ce ya riga ya faɗa wa Uba Sani tun kafin zaɓe cewa zai ba shi cikakken ‘yanci bayan nasara.

El-Rufa'i ya ce bai san abin da ya faru a Kano ba
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tare da Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Game da siyasar Kano, ya ce ba za a kwatanta rikicin Kaduna da wanda ake zargin ya faru a Kano, El-Rufai ya ce a yi hattara da yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Abba Hikima: Jama'a sun ƙara tara wa Haruna kuɗi bayan kashe matarsa da yara 6

“Yanayi ya bambanta. Idan ba ka san dukkannin gaskiya ba, ka yi jinkiri wajen hukunci."

Ya kara da cewa ba shi da masaniya a kan abin da ya faru a Kano, kuma ba shi da niyyar neman bayani saboda ba sabon al'amari ba ne a siyasa.

Nasir El-Rufa'i ya kara da cewa ba abin mamaki ba ne idan Abba da Kwankwaso suka daidata a nan gaba.

El-Rufa'i ya dura a kan Akpabio

A baya, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi zargin cewa Sanata Godswill Akpabio ne ya hana ruwa gudu a kan dokar zaben kasar nan.

Ya ce ba majalisa gaba daya ce ta ke kokarin hana tabbatar da an aiwatar da dokokin zaben da ake so a sauya ba, nauyin ya rataya a wuyan Shugabanta.

Tsohon gwamnan Kaduna ya yi zargin cewa Akpabio dan amshin shata ne, kuma manyan kasar nan kawai ya ke yi wa aiki ba wai yan Najeriya da ke son canji ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng