Rikicin PDP: Gwamnoni 2 da Manyan Jiga Jigai Sun Dura Kotun Daukaka Kara a Abuja

Rikicin PDP: Gwamnoni 2 da Manyan Jiga Jigai Sun Dura Kotun Daukaka Kara a Abuja

  • A yau Talata, 10 ga watan Janairu, 2026 ne kotun daukaka kara mai zama a Abuja ta shirya zama kan shari'ar da aka shigar gabanta game da rikicin PDP
  • An ga gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Mainse sun halarci zaman kotun a Abuja
  • Jam'iyyar PDP ta jima tana fama da rigingimun cikin gida, wanda ya kai ga darewarta gida biyu, tsagi. wamnoni da bangaren ministan Abuja, Nyesom Wike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rikicin shugabanci da ke ci gaba da daukar hankula a babbar jam'iyyar adawa ta kasa watau PDP ya sake daukar sabon salo yayin da aka dawo zaman shari'a a kotu.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban tsagin jam’iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya jagoranci manyan kusoshin jam'iyyar zuwa kotun daukaka kara mai zama a Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan Abba ya shiga APC, Shugaba Tinubu zai yi aikin titin Naira biliyan 19 a Kano

Gwamna Makinde.
Gwamna Seyi Makinde, Gwamna Bala Mohammed da waus jiga-jigan PDP a kotun daukaka kara Hoto: Bashir Hussaini Maitsada
Source: Facebook

Gwamnoni 2 da suka halarci zaman kotu

Jaridar Leadership ta tattaro cewa daga cikin tawagar Turaki da ta halarci zaman kotun akwai shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo

Wadannan gwamnoni sun halarci zaman kotun daukaka kara da ke Abuja game da shari’ar da je gudana jan akaddamar shugabancin jam’iyyar.

An ruwaito cewa gwamnonin na tare da mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) karkashin jagoranci Tanimu Turaki a zaman shari'ar wanda ke gudana yau Talata, 10 ga watan Janairu, 2026.

Jam’iyyar ta dade tana fama da rikicin shugabanci tsakanin bangaren da ke biyayya ga gwamnonin PDP da kuma bangaren Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike.

Wannan takaddama dai ita ce ta yi sanadin da dakarun ‘yan sanda suka garkame babbar sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa da ke Wadata Plaza a cikin birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Tun kafin a yi nisa, an sauke gwamna daga matsayin shugaban kwamitin taron APC na kasa

Kowane bangare ya kori daya bangaren daga jam’iyyar PDP, sannan suka rushe rassan jam’iyyar na jihohi da ke marawa bangaren adawa baya.

A makon da ya gabata ne babbar kotun tarayya mai zama a Ibadan ta rushe bangaren Turaki, tare da tabbatat da sahihincin bangaren da Abdulrahman Mohammed ke jagoranta, wanda ke samun goyon baya daga Wike.

Sai dai tsagin Tanimu Turaki ya yi fatali da wannan hukuncin, inda ya daukaka kara zuwa kotun da ke gaba, lamarin da ya iara rura wutar rikicin jam'iyyar adawa ta PDP.

Gwamnanonin Bauchi da Oyo, wadanda ake ganin su ke marawa tsagin Tanimu Turaki baya sun halarci zaman kotun daukaka kara ne domin a yi shari'ar a gabansu.

Da gaske INEC ta amince da tsagin Wike?

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zaben Najeriya watau INEC ta bayyana cewa babu wani tsagi da ta amince da shi fiye da dayan a jam'iyyar PDP.

INEC ta bayyana cewa ganin kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP da AbdulRahman Mohammed da Samuel Anyanwu ke jagoranta, a taronta ba shi ke nuna hukumar da dauki bangare daya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262