Hadimin Kwankwaso Ya Tsokani 'Yan APC bayan Abba Ya Tarar da Rikici a Jam'iyyar

Hadimin Kwankwaso Ya Tsokani 'Yan APC bayan Abba Ya Tarar da Rikici a Jam'iyyar

  • Hadimin Rabiu Musa Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ya yi kalamai masu kama da tsokana ga ‘yan APC sakamakon sabanin siyasa da ya bayyana
  • Tsokanar ta zo ne bayan 'yan APC sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki guda biyu a karamar hukumar Birni a Kano maimakon a hadu waje guda
  • Lamarin ya kara tayar da hankula kan makomar hadin kan APC bayan sauya shekawar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC mai mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ya yi tsokaci mai dauke da tsokana kan jam’iyyar APC bayan bayyanar rikicin cikin gida a wasu sassan jihar Kano.

Tsokacin nasa ya biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu ‘yan jam’iyyar APC sun kasa gudanar da taro guda daya na masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Birni.

Kara karanta wannan

APC a Kano: An tsige mutumin Ganduje, 'yan bangaren Barau sun ware sun yi taro

Abdullahi Ganduje Abba Kabir Yusuf
Abdullahi Ganduje ya daga hannun Abba Kabir Yusuf a Kano. Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da hadimin Sanata Rabiu Kwankwaso mai suna Saifullahi Hassan ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Hadimin Kwankwaso ya tabo 'yan APC

A martaninsa da ya wallafa, Alhaji Saifullahi Hassan ya bayyana abin da ya faru a karamar hukumar Birni, inda ya ce an gudanar da taron masu ruwa da tsaki guda biyu.

Ya kuma yi ishara da cewa wasu ‘yan siyasa da suka bar NNPP da hujjar rikicin cikin gida, sun tsinci kansu a jam’iyyar da ke gudanar da tarukan bangarori daban-daban kan batu guda.

Barau Jibrin da Abba Kabir Yusuf
Sanata Barau Jibrin da Gwamna Abba Kabir Yusuf. Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Ga sakon da ya rubuta:

"Mu a Kano Municipal taron masu ruwa da tsaki na APC guda biyu aka yi, kowane bangare sun yi nasu gudun kada a tashi baran-baran.
"Wanda ya ce ya fita daga NNPP saboda rikicin cikin gida, sai ga shi ya zo inda ake taron masu ruwa da tsaki guda biyu saboda wannan bangaren baya shiri da daya bangaren, kowa ya yi nasa."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fita kasar waje, ya yi magana kan sauya shekar Abba Kabir

Rikice-rikicen jam'iyyar APC a Kano

Daily Trust ta wallafa cewa tun da farko, masana harkokin siyasa sun ce sauya shekar Abba Kabir Yusuf zuwa APC na iya janyo sabani tsakanin sababbin shiga da tsofaffin 'yan jam’iyyar.

Duk da cewa an dauki irin wadannan hasashe a baya a matsayin ba komai ba, abubuwan da suka faru a karamar hukumar Birni da Dawakin Tofa sun fara nuna alamun sabani a fili.

Rahotanni sun ce wasu kananan hukumomi sun yanke shawarar shirya tarukan hadin kai domin magance damuwar da ta taso bayan sauya shekar gwamnan, gabanin tarukan jam’iyyar na jiha, kananan hukumomi da mazabu.

Sai dai a karamar hukumar Birni, maimakon taro guda daya, an gudanar da taruka biyu a wurare daban-daban, abin da masu lura da siyasa ke kallo a matsayin alamar rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar APC.

Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Dubai

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai wata ziyara Dubai.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya firgita mutanen Abba Kabir bayan tara dandazon jama'a a Kano

Ya yi amfani da damar wajen ganawa da 'yan Kwankwasiyya da ke zaune a can, wandanda yawancinsu 'yan jihar Kano ne.

Kwankwaso ya yi kira gare su su zama jakadu na kwarai a zaman da su ke a can, yana cewa an san 'yan Kano da dattaku.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng