Atiku ko Obi: El Rufai Ya Yi Maganar Wanda Zai Iya Samun Tikitin Takarar ADC a Zaben 2027

Atiku ko Obi: El Rufai Ya Yi Maganar Wanda Zai Iya Samun Tikitin Takarar ADC a Zaben 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a ADC, Nasir El-Rufai, ya ce jam'iyyar ba za ta yi amfani da tsarin karba-karba wajen tsaida dan takara ba
  • Malam El-Rufai ya ce jam'iyyar ADC ta shirya tsaf a matakin farko kuma ta fara rijistar membobinta kafin gudanar babban taron jam'iyya na kasa
  • Tsohon gwamnan ya ce jam'iyyar ADC ta shirya bayyana wani tsari na shugabanci kuma tana goyon bayan tura sakamakon zabe ta hanyar intanet

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar ADC, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba za su yi amfani da tsarin karba-karba a jam'iyyar hadaka ba.

El-Rufai ya jaddada cewa duk wanda ke da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC zai samu dama, ba tare da takura ko fifita wani yanki ba.

Kara karanta wannan

Sanata ya gama nazari, ya fito takarar gwamna a inuwar APC a zaben 2027

Peter Obi da Atiku.
Manyan jagorori a tafiyar hadaka; Peter Obi, Nasir El-Rufai da Alhaji Atiku Abubakar Hoto: @PeterObi, Nasir El-Rufai, @Atiku
Source: Twitter

ADC za ta bi tsarin karba-karba a 2027?

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da tashar Trust TV a shirin mintuna 30, inda ya yi bayani kan dabarun ADC na fitar da ɗan takararta da kuma yadda jam’iyyar ke shirin karbe mulki daga hannun APC.

A cewarsa, ADC ta yanke shawarar gudanar da zaɓen fitar da gwani na gaskiya kuma a bude, ba tare da tsarin yanki ko tilasta ɗan takara ta hanyar yarjejeniya ba.

“Ba za mu yi amfani da tsarin karba-karba ba, ba za mu bi wannan hanya ba. Kowa zai samu damar tsayawa takara, kuma duk wanda ya yi nasara, kowa zai mara masa baya,” in ji El-Rufai.

Manyan jiga-jigan da ke neman takara a ADC sun hada da tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari, Dalung ya fadi manyan ADC da za su iya kifar da Tinubu a 2027

Jam'iyyar ADC na shirye-shirye a bayan fage

Da yake mayar da martani kan ra’ayin wasu cewa ADC ba ta cika fitowa fili ba duk da ƙorafe-ƙorafen jama’a kan halin da ƙasar ke ciki, El-Rufai ya ce jam’iyyar na yin shirye-shirye ne a hankali, maimakon hayaniya a kafafen yaɗa labarai.

Ya bayyana cewa sabanin APC a shekarar 2014 wadda ta kasance haɗakar jam’iyyu, ADC haɗakar mutane ce, lamarin da ke buƙatar lokaci wajen daidaita tsari da gina ƙaƙƙarfan tubali.

“Akwai ayyuka da dama da ake yi a bayan fage. Ana wayar da kai sosai a matakin ƙasa, ko da yake ba lallai ne a ga komai a kafafen labarai ba,” in ji shi.
Malam Nasir El-Rufai.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @Elrufai
Source: Twitter

El-Rufai ya ƙara da cewa jam’iyyar ADC ta fara rajistar mambobi, sannan za ta gudanar da tarukan zaben shugabanni tun daga mazabu, ƙananan hukumomi, kafin a kai ga babban taron ƙasa.

El-Rufai ya goyi bayan zanga-zanga

A wani rahoton, kun ji cewa Malam Nasir El-Rufai ya nuna goyon bayansa ga zanga-zangar da jagororin 'yan adawa suka gudanar a majalisar tarayya kan dokar zabe.

Kara karanta wannan

Tun kafin a yi nisa, an sauke gwamna daga matsayin shugaban kwamitin taron APC na kasa

Tsohon gwamnan na Kaduna ya kuma bayyana gabar da ake tafka magudin zabe a Najeriya, inda ya nuna muhimmancin tura sakamako ta intanet.

El-Rufai ya ce da yana nan da ya shiga zanga-zangar da suka gudanar a majalisar tarayya kan kin amincewa da tanadin tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo kai tsaye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262