El Rufai Ya Yi Fallasa, Ya Tona Gabar da Ake Yin Magudin Zabe a Najeriya

El Rufai Ya Yi Fallasa, Ya Tona Gabar da Ake Yin Magudin Zabe a Najeriya

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduns, Nasir El-Rufai ya nuna goyon bayansa ga zanga-zangar da jagororin 'yan adawa suka gudanar a majalisar tarayya kan dokar zabe
  • El-Rufai ya bayyana cewa da yana cikin Najeriya da ya shiga cikinsu Peter Obi wajen gudanar da zanga-zangar
  • Tsohon gwamnan ya kuma bayyana gabar da ake tafka magudin zabe a Najeriya, inda ya nuna muhimmancin tura sakamako ta yanar gizo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce da yana cikin Najeriya, da ya haɗu da jagora a jam’iyyar ADC, Peter Obi, da wasu shugabannin jam’iyyu wajen gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya.

El-Rufai ya ce da yana nan da ya shiga zanga-zangar da suka gudanar a majalisar tarayya kan cire tanadin tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo kai tsaye daga dokar zaɓe da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

Sanata ya gama nazari, ya fito takarar gwamna a inuwar APC a zaben 2027

El-Rufai ya yi magana kan shiga zanga-zanga a majalisar tarayya
Malam Nasir El-Rufai a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @ADCVanguard
Source: Twitter

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairun 2026 yayin wata hira da tashar Trust TV.

El-Rufai ya goyi bayan zanga-zanga kan dokar zabe

Tsohon gwamnan ya yi tsokaci kan zanga-zangar da aka yi a majalisar tarayya domin nuna adawa da matakin da majalisar dattawa ta ɗauka na cire tanadin da ke wajabta tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo kai tsaye daga rumfunan zaɓe a sabuwar dokar zaɓe.

Da aka tambaye shi matsayarsa kan batun, El-Rufai ya soki majalisar dattawa bisa hana aiwatar da wani sashe da majalisar wakilai ta riga ta amince da shi, yana mai cewa tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta yanar gizo muhimmin ginshiƙi ne wajen tabbatar da sahihancin zaɓe.

“Abin takaici ne cewa ban samu damar dawowa Najeriya ba. Da ina nan, da na haɗu da Peter Obi da sauran shugabannin jam’iyyu wajen yin zanga-zanga a majalisar tarayya domin a dawo da tanadin tura sakamakon zaɓe kai tsaye kuma tilas daga rumfunan zaɓe."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Gwamna Bala ya fatattaki kwamishinan Bauchi daga aiki

- Nasir El-Rufai

Me El-Rufai ya ce kan magudin zabe?

Tsohon gwamnan ya ce maguɗin zaɓe a Najeriya ba ya faruwa a rumfunan zaɓe, sai dai a cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

“Wannan ita ce kaɗai hanyar da za a iya dakatar da maguɗin da ake yi a cibiyoyin tattara sakamako. A can ne ainihin maguɗin ke faruwa. Ba a yin maguɗin zaɓe a rumfunan zaɓe; a cibiyoyin tattara sakamako ake yin sa."

- Nasir El-Rufai

Ya nuna damuwa cewa duk da majalisar wakilai ta amince da tanadin, majalisar dattawa na ci gaba da hana aiwatar da shi, yana mai cewa idan aka aiwatar da tanadin, zai kara inganta sahihanci da amincin zaɓubbukan Najeriya.

“Wannan tanadi da majalisar wakilai ta amince da shi, amma abin takaici majalisar dattawa na hana aiwatar da shi, da ya inganta ingancin zaɓubbjkanmu sosai."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya yi magana kan magudin zabe
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

El-Rufai ya zargi gwamnatin APC

El-Rufai ya kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da kuma gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da adawa da tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo saboda dalilai na siyasa.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun mamaye Majalisar Dattawan Najeriya, sun bayyana bukatarsu

“Amma duk mun san dalilin da ya sa jam’iyya mai mulki da gwamnatin da ke kan mulki ba sa son hakan, domin sun san ba za su iya cin zaɓe ba."
"Hanya ɗaya tilo da za su samu dama ita ce su iya yin maguɗin sakamako bayan mutane sun kaɗa ƙuri’a. Don haka da ina nan, da na shiga zanga-zangar tare da su."

- Nasir El-Rufai

An bukaci Tinubu ya dawo da El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Malam Salisu Isa Nataro, ya ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara.

Malam Salihu ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki mataki cikin gaggawa domin dawo da Nasir el-Rufai cikin jam’iyyar APC.

A ccewarsa, El-Rufai na da tasiri sosai a tsakanin masu ruwa da tsaki a Arewa maso Yamma, kuma hakan na iya taimaka wa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng