Bayan Pantami, Malamin Musulunci Ya Magantu kan Takarar Gwamna a Borno

Bayan Pantami, Malamin Musulunci Ya Magantu kan Takarar Gwamna a Borno

  • Fitaccen malamin Musulunci a Borno, Sheikh Muhammad Mustapha, ya yi magana kan rade-radin cewa yana shirin tsayawa takarar gwamna
  • Sheikh Mustapha ya ce hotunan da ake yadawa a kafafen sada zumunta ba shi ya kirkire su ba, kuma ba ya da niyyar shiga siyasa
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake ta maganganu bayan Farfesa Isa Ali Pantami ya nuna sha'awar neman takarar gwamna a Gombe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Fitaccen malamin Musulunci a Borno, Sheikh Muhammad Mustapha ya yi karin haske game da rade-radin tsayawa takara.

An yi ta yada wasu hotunan Sheikh Modu Mustapha da ke nuna zai nemi takarar gwamna a jihar Borno.

Malamin Musulunci ya musanta rahoton cewa zai nemi gwamna a Borno
Malamin Musulunci a Borno, Sheikh Muhammad Mustapha. Hoto: Sheikh Muhammad Mustapha Albarnawi.
Source: Facebook

Martanin Sheikh Modu Mustapha kan 'neman gwamna'

Malamin ya bayyana gaskiya kan lamarin a jiya Lahadi 8 ga watan Fabrairun 2026 da muke ciki a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Abba Kabir ya yi ga wadanda suka yi hatsari a Kano bayan jajanta musu

Shehin malamin ya musanta rahoton da ake yadawa inda ya ce ko kadan babu wani shiri da yake yi na neman takara a zaɓen 2027 da ke tafe.

Sheikh Mustapha ya ce ya samu labarin yada hotunansa wai zai nemi takarar gwamna inda ya ce ba shi ne a gabansa ba.

Bangaren da malamin ya mayar da hankali

Shehin malamin ya ce yanzu ya mayar da hankalinsa ne kan koyarwar addinin Musulunci domin taimakawa al'umma baki daya saboda samun tsira a lahira.

Ya ce:

"Da yammacin yau (Lahadi) ne na samu labarin da ke yawo cewa wai ina shirin tsayawa takarar gwamnan Jihar Borno.
" Ina sanar da jama’a cewa ba ni da wani shiri ko niyya na tsayawa takara. A halin yanzu, hankalina ya karkata ne gaba ɗaya kan abin da nake yi, wato tafsiri da koyar da addinin Musulunci.
"Zan ci gaba da yin abin da nake yi domin amfanin al’umma, wato wa’azi da koyar da abin da Allah ya umarta a Musulunci."
Sheikh Modu Mustapha ya magantu kan jita-jitar neman gwamna
Malam Muhammad Mustapha daga jihar Borno. Hoto: Sheikh Muhammad Mustapha Albarnawi.
Source: Facebook

Shawarar da Sheikh Mustapha ya ba al'umma

Sai dai malamin ya nuna damuwa kan yadda mutane ke zama su tsara irin wadannan rahotanni kan takarar gwamna da aka ce zai yi duk da cewa babu kamshin gaskiya a tare da su.

Kara karanta wannan

Ana zargin yaran Turji sun yi ajalin liman da basarake, jama'a sun tarwatse

Sheikh Modu Mustapha ya roki al'umma da su yi watsi da rahoton da ake yadawa wanda kwata-kwata ba gaskiya ba ne inda ya bukaci mayar da hankali kan abubuwa masu amfani.

"Don haka, ina roƙon jama’a su yi watsi da irin waɗannan rubuce-rubuce da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta. Bissalam."

- Sheikh Muhammad Mustapha

Pantami ya shiga siyasa gadan-gadan a Gombe

A baya, mun ba ku labarin cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Gombe domin sabunta rajistarsa ta zama mamba.

Tsohon Ministan na sadarwa a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya dade yana shiga cikin harkokin siyasa.

Farfesa Pantami ya kuma bayyana shawarar da ya taba samu daga wajen tsohon shugaban kasar na Najeriya kan siyasar Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.