Gwamnan Borno ya jagoranci Tawaga sun ziyarci Dangin Abba Kyari a Bama

Gwamnan Borno ya jagoranci Tawaga sun ziyarci Dangin Abba Kyari a Bama

Kwanaki biyu da rasuwar babban hadimin shugaban Najeriya, mai girma gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya jagoranci jami’an gwamnati zuwa ta’aziyya ga dangin marigayin.

Farfesa Babagana Umara Zulum da wasu manya a gwamnatin jihar Borno sun je babban gidan marigayi Malam Abba Kyari domin yi masu ta’aziyya game da babban rashin da kasar ta yi.

‘Danuwan marigayin Baba-Shehu Zannah Arjinoma, shi ne ya tarbi gwamnan na jihar Borno da gayyarsa da ta hada da sanatan yankin kudancin jihar Borno watau Mohammed Ali Ndume.

Akwai sakataren gwamnatin jihar Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa, da mai ba gwamna Babagana Zulum shawara a kan harkar addini watau Sheikh Modu Mustapha cikin tawagar.

Alhaji Baba-Shehu Zannah Arjinoma wanda shi ne babban kanin marigayi Abba Kyari shi ne ke rike da sarautar kauyen Banki, Banki wani kauye ne da ke kan iyakar karamar hukumar Bama.

KU KARANTA: Bayanai game da mutumin da COVD-19 ta kashe a Jihar Borno

Gwamnan Borno ya jagoranci Tawaga sun ziyarci Dangin Abba Kyari a Bama

Babagana Zulum ya ce Kyari ya taimakawa Borno a rikicin Boko Haram
Source: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Abba Kyari ya fito ne daga wani babban gidan sarauta da ke cikin garin Bama, kuma ‘yanuwansa ne ke rike da Kauyen Banki. Bama gari ne da ya yi suna sosai da kasuwanci.

Sheikh Modu Mustapha ne ya jagoranci addu’o’in da aka yi wa Abba Kyari wanda ya riga mu gidan gaskiya. Tawagar ta yi addu’a ga Ubangiji ya gafartawa tsohon hadimin duk zunubansa.

Bayan sun kammala ziyarar ta’aziyyar, ‘yan jarida sun yi magana da gwamnan Borno, Farfesa Zulum wanda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kan-kan da kai mai kokarin aiki.

Zulum ya ce ba kasafai ake samun mutum mai kokari da dagewa bisa aikinsa kamarsa ba. Ya ce sau shida ya na zuwa fadar shugaban kasa ya na samun Kyari a ofis kafin karfe 8:00 na safe.

“Na samu damar ganawa da shi sau shida a cikin wata goma, ya kan bani karfe 8:00 a matsayin lokacin samun shi, amma duk zuwan da na ke yi kafin lokacin, a ofis na ke samun shi.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel