2027: Magoya Baya Sun Matsa, Ana Son Obi da Kwankwaso Su Hadu a Kayar da Tinubu
- Ana kara matsin lamba a cikin da wajen ADC domin hada Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a tikitin takarar shugaban kasa
- Rahotanni sun nuna cewa tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo na mara wa Obi baya, yayin da ake kokarin gina kawancen adawa
- Kungiyar Kwankwasiyya ta fito fili ta goyi bayan tikitin Obi–Kwankwaso a zaben 2027 a shirin da ake yi na babban zabe a Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu manyan ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki na kara kaimi wajen tura kudurin hada tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ana son a tsayar da su matsayin 'dan takarar shugaban kasa da na mataimakin shugaban kasa karkashin jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027 mai zuwa.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa duk da cewa shugabancin ADC na kokarin rage zafin batun, masu goyon bayan kudurin na ci gaba da matsa lamba a kan a yi hadin.
Ana son Kwankwaso da Obi su hade
Trust radio ta wallafa cewa masu goyon bayan tikitin Obi da Kwankwaso suna masu cewa hadin shi ne mafi dacewa da karfin da zai kifar da gwamnatin Tinubu.
Majiyoyi da dama sun shaida wa jaridar cewa wannan yunkuri ya zarce jam’iyya guda, inda ya hada da manyan ’yan adawa, masu fada.
Ana ganin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ba wai kawai yana goyon bayan kudurin ba ne, har ma ana kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan masu mara wa burin Obi baya.

Source: Twitter
Obi da Kwankwaso, wadanda suka tsaya takarar shugaban kasa a 2023 karkashin LP da NNPP, sun taba tattaunawa kan yin kawance kafin zaben, amma hakan ya ci tura.
A zaben 2023, Obi ya samu kuri’u sama da miliyan shida, ya lashe jihohin Kudu-maso-Gabas baki daya, Legas da Abuja.
Shi kuma Kwankwaso ya yi nasara a Kano, daya daga cikin jihohin da ke da mafi yawan masu kada kuri’a a kasar nan.
Obi da Atiku: Jam'iyyar ADC na tattaunawa
Majiyoyi sun ce dalilin sake farfado da tattaunawa a ADC shi ne fahimtar cewa hadin karfin Obi a Kudu da na Kwankwaso a Arewa maso Yamma zai iya sauya akalar siyasa a 2027.
Duk da Obi ya shiga ADC a hukumance, Kwankwaso na nan daram a NNPP, sai dai ya shaida wa magoya bayansa cewa yana tuntubar shugabannin siyasa kafin yanke matsaya.
Wani babban jigo a ADC ya ce ba a tattauna batun Obi–Kwankwaso a matakin jam’iyya, amma ana ta tattaunawa a tsakanin 'yan ADC a kan lamarin.
A bangare guda, kungiyar Kwankwaso Support Group (KSG) ta goyi bayan tikitin hadin gwiwar, tana mai cewa zai kawo karshen rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziki.
Shugaban KSG, Abba Gwale, ya ce hadin Obi da Kwankwaso zai zama barazana ga APC, yana mai jaddada cewa ’yan Najeriya sun gaji da halin da ake ciki.
Obasanjo zai hada Obi da Kwankwaso
A baya, kun ji cewa alamun siyasa sun fara nuna cewa ana sake nazari kan yiwuwar haɗa tsofaffin ’yan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a takarar 2027.
Rahotanni sun ce ana sa ran cewa hadin Obi da Kwankwaso zai kai su ga fafatawa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yayin neman tikitin shugaban ƙasa a ADC.
Sabon yunƙurin ya biyo bayan gazawar yarjejeniyar haɗin gwiwa da aka yi ƙoƙarin cimmawa kafin zaɓen 2023, inda rashin jituwa kan wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


