Dokar Zabe: An Fara Neman a Tsige Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Dokar Zabe: An Fara Neman a Tsige Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

  • An fara sukar shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio kan rashin amincewa da tura sakamakon zabe ta intanet kai tsaye
  • Jigo a jam'iyyar adawa ta ADC, Kenneth Okonkwo, ya bayyana Sanata Akpabio a matsayin makiyin tsarin dimokuradiyya a Najeriya
  • Ya ce dokar zaben da Akpabio ya jagoranci amincewa da ita a Majalisar dattawa ta cancanci a tsige shi daga mukaminsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce da kai kawo kan batun gyaran kundin dokar zaben Najeriya, wanda Majalisar dattawa ta yi a makon da ya wuce.

Bangaren da ya fi jan hankali da tayar da kura shi ne batun tura sakamakon zabe ta intanet kai tsaye daga kowace rumfar zabe a fadin Najeriya.

Sanata Godswill Akpabio.
Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio na jagorantar zaman sanatoci a Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Okonkwo ya nemi a tsige Akpabio

A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels tv, Jigo a jam'iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, ya soki Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan

An samu sabani tsakanin Majalisar Dattawa da ta wakilai wajen gyara dokar zaben Najeriya

Okonkwo ya nuna damuwarsa kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan amincewar da Majalisar dattawa ta yi da kudirin gyaran dokar zabe ta 2026, inda ya yi kira da a tsige Akpabio daga mukaminsa.

A cewarsa, matakin da Sanata Akpabio ya jagoranta na barin tsohon tanadin dokar tura sakamako ta intanet, ya nuna cewa shugaban majalisar ya zama maƙiyin dimokuraɗiyya.

Dalilin neman sauke shugaban Majalisa

“Abin da hakan ke nufi shi ne Sanata Godswill Akpabio ya zama maƙiyin dimokuraɗiyya.
"Yana goyon bayan mummunar dabi’ar magudin zaɓe, karkatar da sakamako, ƙirƙira da ruɗani, ta hanyar ƙoƙarin barin tanadin da Kotun Koli ta bayyana cewa duk wanda ya tsaya a kai, maƙiyin dimokuraɗiyya ne.
“Wannan mutumi maƙiyin dimokuraɗiyya ne kuma ya kamata a cire shi daga kujerarsa idan bai yi murabus da kansa ba.”

- In ji Kenneth Okonkwo.

Majalisar Dattawa dai ta amince da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe bayan karatu na uku a makon da ya gabata.

Gyaran da Majalisa ta yi wa dokar zabe

A ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta yanke shawarar barin tanadin sashe na 60, watau tura sakamakon zabe ta intanet yadda yake a cikin Dokar Zaɓe ta 2022, wanda ke bai wa INEC ikon yanke shawara kan yadda za a tura sakamakon zaɓe.

Kara karanta wannan

Abin da Majalisar Dattawa ba ta yarda da shi ba game da tura sakamakon zabe ta intanet

Majalisar ta kuma ƙi amincewa da bukatar wajabta tura sakamakon zaɓe kai tsaye zuwa shafin INEC, haka kuma ta ƙi saka haramcin shiga siyasa na shekara 10 ga masu sayen ƙuri’a.

Kenneth Okonkwo.
Jigo a jam'iyyar hadakar yan adawar Najeriya, ADC, Kenneth Okonkwo Hoto: Kenneth Okonkwo
Source: Twitter

Sai dai ta bar hukuncin daurin kurkuku da tara kamar yadda yake a tsohuwar dokar zaben, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Okonkwo ya shiga jerin wadanda suka nuna bacin ransu kan batun tura sakamako ta intanet, ya ce ya kamata Akpabio ya yi murabus ko a tsige shi.

Akpabio ya yi bayani kan dokar zabe

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Godswill Akpabio ya musanta rahoton cewa Majalisar dattawa ta yi fatali da dokar tura sakamakon zabe ta na'ura kai tsaye.

Akpabio ya bayyana cewa majalisar dattawa ba ta yi watsi da tura sakamakon zabe ta na’ura ba a cikin gyaran da ta yi wa dokar zaben Najeriya.

Shugaban Majalisar dattawa ya jaddada cewa fassarar da mutane suka yi kuskure ne, kuma tura sakamako ta yanar gizo har yanzu yana cikin dokar kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262