Zaben 2027: An Ba Shugaba Tinubu Mafita kan Yadda zai Yi da Kashim Shettima
- An yi ta yawo da jita-jitar cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na iya sauya Kashim Shettima daga matsayin abokin takararsa a zaben 2027
- Har ya zuwa yanzu dai Shugaba Tinubu bai yi magana kan lamarin ba, amma shugaban APC na kasa ya musanta jita-jitar
- Wani mai goyon bayan shugaban kasa ya ba shi shawarar abin da ya kamata ya yi wa Kashim Shettima a zaben shekarar 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu shawara kan yin takara tare da Kashim Shettima a zaben 2027.
An shawarci Shugaba Tinubu da kada ya cire Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Twitter
Wani jagoran 'yan Arewa da ke zaune a Kudu, Alhaji Musa Saidu, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan
Atiku Abubakar ya fito ya yi magana bayan Aisha Buhari ta kai masa ziyara a Saudiyya
Wace shawara aka ba Tinubu kan Shettima?
Alhaji Musa Saidu ya ce bai kamata shugaban kasa ya mika wuya ga matsin lambar sauya mataimakinsa ba, yana mai gargaɗin cewa yin hakan na iya rage masa goyon baya a Arewa.
“Idan cire mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai jawo wa shugaban kasa matsala, to ya fi dacewa ya bar shi a matsayin mataimaki."
"Cire Shettima ba kyakkyawar dabara ba ce a siyasa ga shugaban kasa. Wannan ita ce shawarata ta gaskiya.”
- Alhaji Musa Sa'idu
An bukaci Tinubu ya yi taka tsan-tsan
Alhaji Musa Saidu, wanda ya ce shi babban mai goyon bayan shugaban kasa ne, ya kuma shawarce shi da kada ya dogara kacokan ga alkawuran da wasu gwamnoni da shugabannin jam’iyya daga Arewa ke yi masa.
A cewarsa, wasu daga cikin gwamnoni da shugabannin jam’iyyar da ke ikirarin cewa suna da karfin siyasa a Arewa ba su da irin wannan karfin a zahiri kamar yadda suke bayyanawa a kafafen yaɗa labarai.
“Muna magana ne saboda muna son shugaban kasa. Mu muna tare da mutane, mun san yadda jama’a ke ji."
"Abin da wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC ke faɗa masa ba lallai ba ne ya zama gaskiya. Abin da suke gaya masa daban da wanda suke gaya mana."
“Kada shugaban kasa ya dogara da abin da shugabannin jam’iyya ke faɗa masa a Arewa. Idan ya yi haka, sakamakon zai iya ba shi mamaki. Ina matuƙar sha’awar a sake zaɓen shugaban kasa, shi ya sa nake magana."
- Alhaji Musa Saidu

Source: Facebook
Tiubu ya samu shawara kan magoya bayansa
Alhaji Musa Saidu ya kuma gargaɗi shugaban kasa da kada ya katse alaƙa da tsofaffin magoya bayansa a faɗin ƙasar nan saboda wasu gwamnoni sun shigo jam’iyyar APC.
"Ka da ya daina alaka da magoya bayansa na ainihi a fadin kasar nan saboda wasu gwamnoni sun shigo APC."
“Ya kamata ya ci gaba da hulɗa da sanannun magoya bayansa, domin wasu daga cikin gwamnonin da suka shigo APC na iya yin abin da zai ba shugaban kasa mamaki."

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Abin da Buhari ya gayawa gwamnonin Arewa kan 'dan takararsa a zaben 2023
- Alhaji Musa Saidu
Tinubu zai je ziyara kasar Birtaniya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci kasar Birtaniya a watan Maris na shekarar 2026.
Shugaba Bola Tinubu dai ya amsa gayyatar da Sarki Charles ya yi masa domin kai ziyarar aiki zuwa kasar Birtaniya.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da cewa wannan ita ce ziyarar aiki ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37.
Asali: Legit.ng
